Mayakan Boko Haram sun kashe makiyaya 17 tare da sace shanunsu da dama, bayan arrangamar da suka yi a Jihar Borno.
Wani yanki da ke wajen garin Damasak da ke jihar Borno a yankin arewa maso Gabas.
- Wang Yi Ya Yaba Da Ayyukan Diflomasiyyar Kasar Sin A Shekarar 2022
- Ba Zan Yi Kewar Barin Mulki Ba Saboda Kushe Ni Da ’Yan Nijeriya Ke Yi Duk Kokarina —Buhari
Jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, ‘yan Boko Haram din sun kai farmakin ne tun a ranar Asabar da ta gabata, a daidai lokacin da makiyayan ke gadin dabbobinsu kusa da kauyen Airamne da ke yankin Mafa, inda bayan fafatawa tsakanin bangarorin biyu, 17 daga cikin makiyayan suka rasa rayukansu.
Jami’an sun ce makamai da kuma adadin mayakan na Boko Haram ya zarce na makiyayan sosai.
Daya daga cikin jami’an tsaron sa-kai a Borno, Ibrahim Liman ya ce ‘yan ta’adddan na Boko Haram sun kaddamar da harin na ranar Asabar ne daga dajin Gajiganna, inda suka koma da zama a bisa tilas, bayan da hara-haren mayakan ISWAP da na sojojin Nijeriya suka kore su daga dajin Sambisa.
A shekarar 2016, ISWAP ta balle daga cikin Boko Haram, daga bisani kuma ta fi karfi a rikicin Arewa Maso Gabashin Nijeriya, inda hakan ya ba ta damar kwace akasarin yankunan da a baya suke karkashin Bokok Haram bayan kashe shugabanta Abubakar Shekau a cikin watan Mayun 2021.
Mayakan Boko Haram da na ISWAP sun dade suna kai hare-hare kan fararen hula da suka hada da masu saran itatuwan katako, manoma da kuma makiyaya, bisa zarginsu da yi wa jami’an tsaron Nijeriya leken asiri.