Wasu da ake zargin ‘yan tada kayar bayan Boko Haram ne, sun sace fasinjoji a babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Majiyoyi sun shaida wa LEADERSHIP cewa mayakan sun tare hanyar garin Kuturu da kauyen Mannanari kusa da Auno, wanda ke kan babbar hanyar Damaturu da misalin karfe 5:50: na yammacin ranar Litinin.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Kari Sansanin Sojoji A Neja
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Abuja Zuwa Nasarawa
Rahotanni sun bayyana cewar sun tare babbar hanyar ne kafin daga bisani suka yi awon gaba da wasu fasinjoji.
Lamarin ya sanya daruruwan matafiya da masu ababen hawa neman mafaka a kan hanyar.
“Wani al’amari ya faru tsakanin Mannanari da Garin Kuturu inda wasu mayakan Boko Haram suka tare motoci tare da sace wasu fasinjoji.
“Ba mu da tabbacin adadin wadanda aka sace amma tabbas an yi garkuwa da mutane a yammacin ranar Litinin.”
Mazauna yankin sun ruwaito yadda direbobi da yawa ne suka fake a kauyukansu lokacin da ‘yan ta’addan suka tare hanyar kauyukan Garin Kuturu da Mannanari.
“Sun fito da wilbaro guda uku kuma ina kyautata zaton neman kayan abinci suka fito. Ba mu san adadin mutanen da aka sace ba amma wasu direbobi sun dawo sun koma Maiduguri kafin sojoji suka isa wajen.”
Wani fasinja da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce shi da wasu fasinjoji sun shafe sa’o’i a tsaye kafin su wuce.
“Muna kan hanyar zuwa Kano daga Maiduguri lokacin da direbanmu ya samu labarin an tare hanyar,” in ji shi.
“Mun dade muna jiran sojoji su bude hanya amma ba mu san yaushe za su zo ba. Muna tsaye a nan.”