Aƙalla mutane 61, ciki har da mutanen gari da sojoji, sun rasa rayukansu a daren ranar Juma’a lokacin da Boko Haram suka kai hari kauyen Darul Jamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, Jihar Borno.
Majiyoyi sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare har zuwa safiyar ranar Asabar.
- Jami’ar IMF Ta Yaba Da Kwararan Bayanan Tattalin Arziki Da Manufofin Kasafin Kudi Na Kasar Sin
- Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa
Maharan sun kashe mazauna ƙauyen da matafiya.
Darul Jamal na kusa da garin Banki.
Mutanen ƙauyen sun dawo ne wannan shekarar bayan dogon lokaci da suka shafe suna zaman gudun hijira.
Yawancin waɗanda aka kashe sun fito ne daga sansanin ’yan gudun hijira da ke Makarantar Sakandare ta Kimiyya ta Gwamnati.
Wata majiyar ta ce: “Aƙalla mutanen gari 56 da sojoji biyar aka kashe. An ƙone gidaje fiye da 20 da kuma motoci 10. Har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.”
Har yanzu, babu wata sanarwa da hukumomi suka fitar game da harin.
A ranar Asabar, Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Bama domin samun cikakken bayani da kuma jajanta wa waɗanda abin ya shafa.
A shekarar 2004, Boko Haram ta mamaye garin Bama tare da ayyana shi a matsayin wani ɓangare na “daularsu” kafin daga baya dakarun sojin Nijeriya suka ƙwato garin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp