Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a.
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji
Al’ummomin da aka kudiri niyyar sake tsugunar da su sun hada da Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram da Darajamal.
Zulum ya ce ana kafa matsugunan tanti na wucin gadi guda 1,000 a kowace al’umma, inda tuni aka kammala wacce ke Darajamal.
“Mun himmatu wajen mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu na asali, a yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da ayyukan a Mayanti, Goniri, Bula Kuriye da kuma Abbaram.
“An kammala Darajamal. Ana haka gololo a kewayen wadannan al’ummomi don inganta tsaro,” in ji Zulum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp