Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da kakkausar murya ya karyata wani rahoton da ke cewa yana da hannu wajen cire dala miliyan 6.3 daga babban bankin Nijeriya (CBN) ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Rahoton wanda wata jarida ta yanar gizo ta buga, ya yi ikirarin cewa wani mai bincike na musamman da shugaba Bola Tinubu ya nada ne ya bankado satar da ake zargin an yi a ranar 8 ga Fabrairu, 2023 — makonni kafin zaben shugaban kasa.
- Badakala: Majalisar Wakilai Ta Bayar Da Umurnin Cafke Gwamnan CBN, Babban Akanta Na Kasa Da Sauransu
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas: Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
Rahoton ya ci gaba da cewa, Mustapha tare da tsohon gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, sun ba da izinin fitar da kudaden daga asusun bankin da nufin bayar da kudaden gudanar da ayyukan sa ido kan zabe na kasashen waje.
Rahoton mai binciken, kamar yadda jaridar ta ruwaito, ta ce na’urar leken asiri ta bidiyo (CCTV) sun dauki bidiyon yadda aka fitar da kudaden daga harabar bankin.
Sai dai Mustapha, a wani kakkausan lafazi da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar, ya musanta zargin da ake masa.
Ya bayyana labarin a matsayin “ƙirƙira” da nufin bata sunansa.