A karon farko wata kasa daga kudancin Amurka za ta karbi bakuncin gasar kofin duniya ta mata da hukumar FIFA ke gudanarwa bayan da aka zabi Brazil ta karbi bakuncin gasar 2027 a taron FIFA da a kayi a ranar Juma’a.
Bayan nasarar da kasashen Australia da New Zealand suka samu a bara, mambobin FIFA sun zabi Brazil a yunkurin fadada wasan kwallon kafa na mata zuwa sabbin nahiyoyi.
- Tinubu Ya Kaddamar Da Gangami Yakin Neman Ilimi
- Duk Ɗan Nijeriya Da Ke Amfani Da Shafukan Intanet Na Shan Aƙalla Datar 9G Kowonne Wata
Wakilan FIFA 197 da suka gudanar da taro a birnin Bangkok sun kada kuri’a, inda 119 suka zabi Brazil domin karbar bakuncin gasar kofin duniya ta mata karo na 10, inda ta doke kasashen Belgium da Netherlands da kuma Jamus.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil, Ednaldo Rodrigues ya yaba da wannan mataki inda ya kira hakan da nasara ga kwallon kafa na Latin Amurka da kuma kwallon kafa na mata a Latin Amurka.