Ga duk mai bibiyar yanayin ci gaban da ake samu karkashin hadakar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen BRICS, zai tabbatar da cewa kungiyar ta haifar da kyakkyawan fatan cimma moriyar juna, matakin da ke kara kyautata moriyar kasashen Afirka, da sauran kasashe masu tasowa.
Kungiyar BRICS mai kunshe da kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta kudu, wadda a yanzu ke shirin karkare taron shugabanninta karo na 15 a Afirka ta kudu, ta tabbatar da matsayinta na adawa da ra’ayin cacar baka, da danniya, ta kuma mai da hankali ga yayata akidun gudanar da cudanya tsakanin dukkanin sassa, da martaba juna, da hadin gwiwa, da rike gaskiya da adalci, ta hanyar samar da wani ginshiki na daban, wanda duniyar yau za ta iya dogaro da shi.
Ya zuwa yanzu, kasashe mambobin kungiyar BRICS ne ke da sama da kaso 40 bisa dari na jimillar adadin al’ummar duniya, da kaso 20 bisa dari na darajar cinikayyar duniya, yayin da kasashe mambobin take janyo kaso 25 bisa dari na daukacin jarin waje da ake zubawa a duniya.
La’akari da alakar kut da kut ta cinikayya, da musaya tsakanin dukkanin wadannan kasashe mambobin BRICS da kasashen nahiyar Afirka, da kuma tasirin alkaluman tattalin arzikinsu ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya, za mu iya gane dalilan da suka sanya ci gaban BRICS ke taka rawar gani ga ci gaban Afirka, ta hanyoyi masu yawa.
BRICS ta riga ta gabatarwa duniya wata dama ta cimma alherai, musamman ga kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa, da kasashe masu tasowa, ta kuma ingiza hadin gwiwarsu, tare da zama wani muhimmin dandali na kyautata ci gaban kasashe masu tasowa ta fuskar dinke dukkanin sassa, yayin tafiya kan tafarkin bunkasuwa tare.
Wadannan dalilai ne suka sanya a halin yanzu, karin kasashen Afirka da suka hada da Najeriya, da Aljeriya da Masar, suka shiga cikin jimillar kasashe 23 dake fatan zama sabbin mambobin wannan kungiya mai daraja.
Yayin da wasu kasashen duniya ke aiwatar da matakan haifar da baraka ga duniya, da kafa tsarin rarrabuwar kawuna, da fadada jibge sojoji, da kafa kawance a fannin, da nufin tabbatar da ikon kashin kai, a hannu guda kungiyar BRICS, na kara mayar da hankali ga bunkasa zaman lafiyar duniya, da yayata manufofin ci gaban bai daya na kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka.
Don haka dai muna iya cewa, yayin da kasashen Afirka ke fafutukar raya kansu, da kaucewa duk wani yanayi na koma baya, kungiyar BRICS ta zama wata hanya mai inganci da kasashe na Afirka za su ci gaba da bi, domin kaiwa ga tudun mun tsira. (Saminu Hassan)