An bude taron al’umma irinsa na farko na kungiyar kasashen BRICS, jiya Litinin a birnin Rio De Janeiro na kasar Brazil, da zummar fadada shigar al’ummomin kasashe mambobin kungiyar cikin harkokin jagorantar duniya da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Shawarar kafa kungiyar BRICS da kasar Sin ta gabatar, abu ne da ya samar wa duniya wata sabuwar alkibla game da yadda ya kamata a sauya akalar tafiyar da harkokin duniya, ta yadda a wannan lokaci mai sarkakiya da tasowar kasashe da dama, kasashe masu tasowa za su rika dogaro da kansu wajen samun ci gaba. Abun nufi shi ne, kungiyar BRICS ta zama murya mai karfi da za su rika magana da ita yayin da suke shiga ana damawa da su a harkokin duniya.
Wannan taro, ya hada kungiyoyin al’umma na kasashen kungiyar, domin su tattauna kan batutuwan da suka shafi hadin gwiwar tattalin arziki da cudanyar kasa da kasa da siyasar duniya da kalubalen shugabanci da hanyoyin rage dogaro da takardan kudi na dala.
Shin kun san rawar da hakan zai iya takawa ga kyautata dangantakar kasashen? Wannan ba ya rasa nasaba da sirri na musamman na ci gaban kasar Sin. Watau jin ra’ayin jama’a da sanya muradu da jin dadinsu gaba da komai. Gwamnatin kasar Sin, gwamnati ce ta jama’a dake sauraron jama’a da kuma hidimta musu. Irin wannan ci gaba na Sin sauran kasashen BRICS za su samu daga tattaunawa tsakanin wakilan kungiyoyin al’umma. Wannan muhimmiyar dabara ce da za ta iya taka rawa wajen kai wa ga dunkulewar al’ummomin kasashe masu tasowa lamarin da zai kara fahimtar juna da karfafa dankon zumunci a tsakaninsu ta yadda kasashen za su rika magana da murya daya.
Bisa la’akari da batutuwan da za a tattauna, shugabannin kungiyar za su ji ainihin ra’ayoyin jama’a game da yadda za su tsara manufofin da za su dace da kyautata musu, ta yadda za su samu ci gaba, haka kuma kungiyar za ta kara samun aminci da karbuwa tsakanin al’umma.
Tabbas kungiyar BRICS ta zo da sabon salon jagorantar harkokin duniya da ya dace da zamani, wanda kuma ya bambanta da tsarin babakere da mamaya. An ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi. Tabbas dabarar inganta hadin kai da fahimta da mu’amala tsakanin kasashe masu tasowa, zai ba su karfin tunkara da yaki da duk wani mai cin zali da neman mulkin danniya. (Fa’iza Mustapha)














