Babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ruben Amorim ya ce ya shaida wa Bruno Fernandes cewa ba zai bar shi ya bar kungiyar ba a bazara, kyaftin din kungiyar Fernandes wanda ya rattaba hannu a kan kwantiragin har zuwa 2027 a watan Agustan da ya gabata ya kasance tauraron dan wasan United a kakar wasa ta bana.
Bruno Fernandes ya ci kwallaye 95 a wasanni 277 da ya buga tun zuwansa Manchester United daga Sporting a shekarar 2020, a karshen mako rahotanni sun bayyana ana danganta dan wasan mai shekaru 30 da komawa Real Madrid.
- Spain Ta Lallasa Ingila A Wasan Ƙarshe Na Kofin Euro 2024
- De Bruyne Zai Bar Manchester City A Ƙarshen Kakar Wasanni
“A’a, ba zai faru ba,” in ji Amorim, lokacin da aka tambaye shi game da jita-jita a wani taron manema labarai kafin buga wasa a gasar Premier ranar Talata da Nottingham Forest, da aka tambaye shi ta yaya zai tabbata haka, tsohon kocin na Sporting ya kara da cewa: “Ba zai je ko’ina ba saboda na riga na fada masa'”.
Fernandes ya zura kwallaye 16 a dukkan gasa a kakar wasa ta bana yayin da babu wani dan wasan United da ya jefa adadin wadannan kwallaye a bana, a mako na karshe kafin hutun kasa da kasa na baya-bayan nan, Fernandes ya zura kwallaye biyar, ciki har da ha-trick a gasar cin kofin Europa da suka doke Real Sociedad.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp