Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF), ta bayyana Bruno Labbadia a matsayin sabon mai horar da tawagar Super Eagles ta Nijeriya.
Labbadia, mai shekara 58 a duniya, ya buga wasa a kungiyoyi irin su Darmstadt da Humberg da Bayern Munich da Cologne a baya, sannan ya koyar da kungiyoyin Hertha Berlin da Stuttgart da Liverkusen da sauransu.
- An Kama ‘Yan Shi’a 97 Kan Kisan ‘Yansanda 2 Abuja
- Gwamnan Nasir Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Naira Biliyan 6.5 Ga Mutane 65,000 A Kebbi
Shi ne mai koyarwa na shida daga ƙasar Jamus da Nijeriya ta dauka, inda a baya masu koyarwa irin su Karl-Heinz Marotzke da Gottlieb Goller da Manfred Honer da Berti Vogt da Gernot Rohr suka koyar da tawagar ta Super Eagles.
Sabon mai horarwar zai fara jagorantar Nijeriya a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka da Super Eagles za ta fafata da ƙasashen Benin da Rwanda a watan Satumba mai zuwa.
Sai kuma a watannin Oktoba da Nuwamba inda zai sake buga wasannin.
A kwanakin baya ne dai Nijeriya ta raba gari da Finidi George, a matsayin mai horaswa watanni kaɗan bayan ya karbi aikin, sakamakon rashin tabuka abin a zo a gani a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka.