Gwamnatin Birtaniya (UK) ta yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya na dawo da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu Nijeriya domin ya kammala tsawon shekarun da aka yanke masa na zaman gidan yari.
A halin yanzu, Ekweremadu yana zaman gidan yari a Birtaniya saboda hada baki wajen cire kodar wani matashi.
- Ya Dace A Binciki Yadda Aka Kwashe Sojoji Masu Gadin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi – Gwamna Nasir
- ‘Yan Ƙunar Baƙin Wake Sun Kashe Jami’ai 3 A Hedikwatar Rundunar Tsaro Ta Pakistan
An yanke masa hukunci a watan Maris na 2023, inda aka yanke masa hukuncin shekaru tara da watanni takwas.
A farkon watan Nuwamba, Shugaba Bola Tinubu ya aika da wata babbar tawaga zuwa Landan don tattauna shari’ar Ekweremadu da kuma yiwuwar ya ci gaba da zaman gidan yarinsa a Nijeriya.
Tawagar ta kunshi Yusuf Tuggar, ministan harkokin waje, da Lateef Fagbemi, babban lauyan tarayya (AGF) kuma ministan shari’a.
Duk da haka, jaridar UK Guardian, wacce ta ambato wani jami’in ma’aikatar shari’a (MoJ), ta ruwaito cewa, an yi watsi da bukatar gwamnatin Nijeriya.














