A ranar Litinin, Kamfanin Siminti na BUA ya ƙaddamar da wani shirin horaswa na musamman ga matasa 60 a Sakkwato kan sarrafa manyan injina masu nauyi, da nufin ƙara basira da ƙwarewa a tsakanin al’ummar yankin da kamfanin ke aiki a cikinsa.
Shugaban kamfanin, Injiniya Yusuf Halliru Binji, wanda Aminu Bashir ya wakilta a wajen taron, ya bayyana cewa shirin horon wani ɓangare ne na ƙoƙarin kamfanin wajen tallafawa al’ummar yankin, musamman wajen samar da hanyoyin samun ƙwarewa da aikin yi ga matasa.
- Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA
- BUA Ya Soki Manyan Diloli Kan Dakile Shirin Sayar Da Siminti A Kan Farashi Mai Sauki
Binji ya bayyana cewa kowanne daga cikin matasan 60 da za a horar zai samu alawus na ₦150,000 a kowane wata, na tsawon watanni shida da horon zai gudana. Ya ce kamfanin ya daɗe yana fuskantar ƙalubalen samun ma’aikata daga cikin al’ummar yankin, domin rashin isasshiyar ƙwarewa.
“Lokuta da dama idan muka buɗe damar neman aiki, galibin waɗanda ke cancanta ba ‘yan yankin Sakkwato ba ne. Wannan ya sa muka ƙuduri aniyar basu horo kai tsaye,” in ji shi.
Kamfanin ya jaddada cewa yana da kishin ganin al’ummar da ke kusa da shi sun ci gajiyar ayyukansa, kuma wannan horo na daga cikin shirye-shiryen ci gaba da hadin gwiwa da al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp