Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya roki Majalisar Dattawa da ta amince da nadin mambobin Majalisar Gudanarwa ta hukumar Bunkasa Shiyyar Arewa Maso Gabas (NEDC) guda 12.
A wata sanarwar da Kakakin shugaban kasan, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya roki majalisar ne ta cikin wasikar da ya aike wa shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan mai dauke da kwanan wata 3 ga Mayu, 2023.
- Sudan: Rukuni Na Biyu Na ‘Yan Nijeriya Sun Iso Abuja
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Al’ummar Afirka Ne Ke Da Ikon Tsokaci Kan Hadin-Gwiwar Su Da Kasar Sin
‘‘Bisa dogara da sashin doka bangare na 1, sashi na 2(5)(b) na hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas (NEDC) ta dokar 2017, ina mai gabatar da jerin sunayen mutanen da na zaba na kuma nada su sha biyu (12) da za su kasance mambobin Majalisar Gudanarwa na hukumar NEDC.
‘‘Ya na da kyau Majalisa ta gane cewa wa’adin mambobin Majalisar Gudanarwar hukumar NEDC da ke jagorantar hukumar a halin yanzu zai kare ne a ranar 7 ga watan Mayun 2023,” ya shaida.
Wadanda shugaban ya zaba su ne: Barista Bashir Bukar Baale, a matsayin shugaba, (Arewa Maso Gabas, Yobe), Suwaiba Idris Baba, Darakta mai cikakken iko, sashin kula da harkokin Jin Kai, (Arewa Maso Gabas, Taraba), Musa Umar Yashi, darakta mai cikakken iko a sashin gudanar da mulki da kula da bangaren kudi, (Dan Arewa Maso Gabas ne da ya fito daga jihar Bauchi), Dakta Ismaila Nuhu Maksha, babban darakta Mai cikakken Iko da ke kula da sashin ayyuka, (Arewa Maso Gabas daga jihar Adamawa) da kuma mai-gayya-mai-aiki, Umar Abubakar Hashidu, a matsayin Manajan Gudanarwa kuma babban jami’in gudanarwa (MD/CEO), (Dan Arewa Maso Gabas ne da ya fito daga jihar Gombe).
Sauran sun hada da: Grema Ali, mamba, (Arewa Maso Gabas, Borno), Onyeka Gospel-Tony, mamba, (Daga Kudu Maso Gabas), Hon. Mrs Hailmary Ogolo Aipoh, mamba, (Dan Kudu Maso Kudu), Air Commodore Babatunde Akanbi (Mai ritaya), mamba (Daga Kudu Maso Yamma ), Mustapha Ahmed Ibrahim, mamba, (Daga Arewa Maso Yamma), Hadiza Maina, mamba, (Arewa ta Tsakiya) da kuma Wakili daga ma’aikatar kudi ya tarayya da kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Buhari sai yayi fatan Majalisar za ya yi la’akari da zabinsa tare da amincewa da su.