Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aikewa majalisar dattijai wasika, inda ya bukaci majalisar dattijai da ta tabbatar da sunayen ministocin da aka nada a matsayin wadanda za su maye gurbin Ministocin da suka bar majalisar zartarwa ta tarayya kwanan nan.
Wadanda aka nada a matsayin ministoci bakwai sune Henry Iko, jihar Abia; Umana Umana, Akwa Ibom; Ekuma Joseph, Ebonyi; Goodluck Opiah, Imo; Umar El-Yakub, Kano; Ademola Adegoroye, Ondo, da Odum Odi, Jihar River.
Za su maye gurbin Ogbonnaya Onu, Rotimi Amaechi, Emeka Nwajiuba, Godswill Akpabio, da Ogar, wadanda dukkansu suka yi murabus daga FEC domin tsayawa takara a zaben 2023.
Cikakkun bayanai na nan zuwa daga baya….
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp