Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya ziyarci jihohin Borno da Jigawa a ranar Talata domin jajanta wa wadanda iftila’i ya afka musu a baya-bayan nan.Â
A Jihar Borno, ya yi jaje game da ambaliyar ruwa da ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, sannan a Jigawa, ya ziyarci wadanda gobarar tankar mai ta shafa wanda ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 180.
- Real Madrid: Me Ke Faruwa Ne A Santiago?
- Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Atamfar HaÉ—in Kan Ƙasa Da Tallafin Littafi 50,000 A ZamfaraÂ
Buhari, ya nuna tausayinsa kan mummunan asarar da ambaliyar ta haddasa a Borno, inda ya danganta hakan da sauyin yanayi.
Ya yaba wa hadin gwiwar gwamnatin tarayya da na jihohi a yunkurin taimaka wa al’ummar da lamarin ya shafa.
A lokacin ziyararsa, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno da Shehun Borno sun gode wa Buhari bisa gudunmawar da ya bayar ga jiharsu.
A Jihar Jigawa, Mukaddashin Gwamna Aminu Usman, ya raka Buhari ziyartar wadanda suka jikkata a gobarar tankar a Asibitin Koyarwa da ke Jami’ar Rasheed Shekoni.
Buhari ya yi addu’a ga wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda ke kwance a asibitoci.
Mukaddashin gwamnan, ya gode wa Buhari saboda ziyarar da ya kai da kuma tallafin kudi da ya bayar ga wadanda iftila’in ya shafa.
Hakazalika, ya yaba masa kan tallafin da ya bayar a irin wannan mawuyacin lokaci da jihar ke ciki.