Domin tabbatar da Nijeriya ta ci gaba da rike muhimman mataki da kuma ba shi damar karasa wa’adinsa a matsayin babban jami’i sasheb ‘yansandan kasa da kasa wato (INTERPOL), shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada tsohon mataimakin Sufeto-Janar na ‘yansanda (AIG), Garba Baba Umar, a matsayin babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro da ya shafi hadin guiwar ‘yansandan kasa da kasa da kuma yaki da ta’addanci a ofishin ministan kula da harkokin ‘yansanda.
Da yake amincewa da nadin nasa, shugaba Buhari, kamar yadda sanarwar da Kakakinsa, Mallam Garba Shehu ya nakalto a ranar Alhamis, ya buga misali da yadda Nijeriya ta tsawaita wa tsohon babban jami’i AIG Kamal Subair (Mai ritaya) damar aiki bayan da ya wa’adin aikinsa ya kare a shekarar 2018.
- Shugaba Xi Ya Ziyarci Birnin Cangzhou A Lardin Hebei
- Ma’aikatan Filato Sun Fara Yajin Aiki Kan Rashin Biyan Su Albashi
Kazalika, Buhari ya ce, babban jami’in AIG Umar ya taimaka wa Nijeriya sosai ta hanyoyin daban-daban.
Tare da fatan cewa a cikin shekara daya da ya rage masa zai kara azama da himma, zai kara kwazo wajen samo wa Nijeriya kayan yaki da ‘yan ta’adda, kula da iyakokin, dakile ta’addanci da ‘yan ta’adda a kasar, taimaka wajen ganin Nijeriya ta kara samun muhimman mukamai a sashin ‘yansandan kasa da kasa wato INTERPOL da ma shigar da ‘yan Nijeriya ciki.
Wa’adin aikin AIG Garba Baba Umar zai kare ne a watan Nuwamban 2024, yanzu kuma ya zama babban mashawarci kan lamarin tsaro da zai fara aiki daga ranar 16 ga watan Mayun 2023