Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattijai wasika, inda ya bukaci ta amince masa karbo wani sabon bashi daga bankin duniya har dala miliyan 800.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban daraktan ofishin kula da basussuka na kasa, Ben Akabueze, ya nuna damuwa kan yadda kasar ke fama da bashi, yana mai cewa akwai kalubale kan duk kasar da ke fama da yawan bashi.
Da yake jawabi a Abuja a wani taron bita game da batun cin bashi, ya ce “Da zarar yawan bashin da ake bin kasa ya zarce kashi 30 cikin 100, kasar na cikin matsala amma kuma duk da haka Nijeriya na kara gaba zuwa kashi 100 cikin 100, wannan yana nuna mana irin matsalar da muke ciki na samun karancin wurin karbar bashi a nan gaba.”
A wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta a majalisar a Abuja, ta ce, shugaba Buhari ya ce za a yi amfani da lamunin ne wajen bunkasa shirin samar da rangwame wajen takaita tsadar kayayyakin masarufi da jin dadin rayuwar al’ummar kasa.