Shugaba Muhammadu Buhari ta rantsar da Dakta Mohammed Bello Shehu, a matsayin Shugaban Hukumar Raba dai-dai ta Kasa, wato RMAFC.
Bello, shi ne tsohon sakataren hukumar da Buhari ya rantsar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, kafin a fara gudanar da taron Majalisar Kasa.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocin Uwargidan Gwamnan Osun Hari
- Sin Ta Zama Daya Daga Cikin Kasashen Dake Sahun Gaba A Kirkire-Kirkire
A hirarsa da manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi, ya ce, hukumar za ta ci gaba da taimaka wa gwamnatin shugaba Buhari wajen kara tara kudeden shiga tare da toshe kafofin da kudaden gwamnatin ke zurarewa.
Sabon shugaban ya ci gaba da cewa, aikin babba ne, kuma mun san halin da Nijeriya ke ciki wanda abu ne har da ma a fadin duniya, musamman idan aka yi duba da kasashen Afrika kamar su Afirka ta Kudu, Habasha, Ghana, Masar, ciki har da Nijeriya da ke fuskantar kalubalen tattalin arziki.
Dakta Bello, ya yi nuni da cewa, “Mun fuskanci annobar Korona a baya da shiga cikin matsin tattalin arziki, inda a yanzu kasar Ukraine ke fama da yaki, inda hakan ya shafi kasashen duniya da dama hakan kuma ya shafi raguwar tara kudaden shiga”.
Ya sanar da cewa, idan aka yi duba ga irin nauyin da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya dorawa hukumar wanda ya hada da bibiyar abin da ya kamata ya shiga cikin lalitar Gwamnatin Tarayya, rabar da kudade da biyan Albashin ‘yan siyasa masu rike da madafun iko da na bangaren shari’a kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda ba a sabunta tun a 2008 ya tanadar.