Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin a Daura, jihar Katsina, ya yi roko ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ta sake duba matsayar ta kan yajin aikin da ta dade tana yi.
Ya kuma nuna damuwarsa cewa, tsawon lokacin da kungiyar ta dauka a yajin aikin, tana barazana ga iyalai da tsarin ilimi da kuma ci gaban kasar a nan gaba.
Shugaban wanda ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ‘yan majalisar dokoki da shugabannin siyasa a gidansa lokacin liyafar bikin Sallah, ya ce lamarin ya yi illa ga nutsuwa da kwanciyar hankalin Iyaye da dalibai da sauran wadanda lamarin ya shafa, ya kamata a shiga tsakanin lamarin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa makomar kasar ta dogara ne kan ingancin cibiyoyin ilimi da ilimi, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ta fahimci halin da malaman ke ciki, kuma ya kamata a maida dalibai ajin karatu, za a ci gaba da tattaunawa daga baya.
Gwamnonin APC da suka halarci liyafar bikin Sallar sun hada da shugaban kasa; Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari; Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai; Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma; Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello; Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Gwamnan Jihar Ekiti, Dr Fayemi Kayode; Gwamnan Jihar Fulato, Simon Lalong da Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.