Shugaba Buhari ya kara kira ga Shugabanni tsaron Nijeriya da su kara kaimi wajen magance Matsalar tsaron da ta addabi sassan Nijeriya daban-daban.
Buhari ya yi kiran ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce dole sai hukumomin tsaro sun kara kaimi za a iya kawo karshen ayyukan ta’addanci da na ‘yan bindiga.
“‘yan Ta’adda da ‘yan bindigar za su dandana kudar su nan ba da jimawa”, inji wani bangare na sanarwar. Kamar yadda BBC ta rahoto.
Talla
Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya addu’ar samun damina mai albarka.
Talla