Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar sabon kamfanin mai na kasa wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa.
An yi kaddamarwar ne a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Abuja.
Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ”mai dimbin tarihi”.
A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga ‘yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makamashin da take bukata.
Ya kuma kara da cewa ”Daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar ‘yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makamashi a fadin duniya”.
”A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Nijeriya wadataccen makamashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makamashin”. in ji Buhari.