Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta kori ɗalibai 29 da dakatar da wasu uku bayan da aka same su da laifin magudi a jarrabawa a shekarar karatu ta baya. Haka kuma, jami’ar ta dakatar da dalibai uku na tsawon zango ɗaya ko biyu yayin da ta wanke wasu uku daga zargin da ake musu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan riƙon Kwarya a sashin shirya Jarrabawa da adana bayanai, Aminu Kurawa ya fitar, kuma aka ba wa jaridar LEADERSHIP, ya shaida cewa ɗalibai daga matakin digiri na farko da kuma na gaba sun kasance cikin wannan hukunci.
- Harin Gwoza: Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Dakile ‘Yan Ta’adda Duk Inda Suke
- ‘Yan Majalisu Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Aiwatar Da Yarjejeniyar Samoa
“Majalisar Zartarwar jami’ar a zaman ta na 413 da aka yi a ranar 3 ga Yuli, 2024, ta kori ɗalibai 29, ta dakatar da uku kuma ta gargaɗi wasu 15 saboda samun su da laifin magudi a jarrabawa.
“An yanke wannan hukunci ne bisa ƙa’idojin jarrabawa da dokokin Karatu (GEAR) da kuma dokokin karatun Digiri na Gaba (GRGPS),” sanarwar ta bayyana.