Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ta aiwatar da tsattsauran mataki kan ɗaliban da aka samu da laifin satar jarrabawa, inda ta kori 62, tare da dakatar da 17 kamar yadda Ƙa’idojin dokokin jarrabawa da karatu na jami’a (GEAR), suka tanada.
An yanke wannan hukunci ne yayin zaman majalisar dattijan jami’ar karo na 421, da ya gudana a ranar 26 ga watan Fabrairu 2025, bayan tabbatar da ɗaliban sun aikata laifuka daban-daban na satar jarrabawa da sauran ayyukan rashin gaskiya.
- Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
Cikin rahoton sanar da korar wanda ke ƙunshe a jaridar mako-mako ta jami’ar, ta bayyana cewa matakin na daga ƙoƙarin BUK na kare darajar ilimi da tabbatar da bin ƙa’idojin jarrabawarta.
Baya ga korar, jami’ar ta dakatar da wasu ɗalibai 17 na wani taƙaitaccen lokaci a matsayin ladabtarwa, inda aka wanke wasu ɗalibai 5 bayan bincike ya tabbatar da ba su da laifinsu.
Kazalika an gargadi ɗalibai 29 kan munin aikata laifin satar jarrabawa, wanda ke nuna matsayar BUK na rashin sassauci kan irin waɗannan laifuka, kana an ɗage yanke hukunci kan wasu ɗalibai uku domin ci gaba da nazari da kuma tattara ƙarin hujjoji kafin a hukuncin ƙarshe.
Daga ƙarshe sanarwar ta ƙara jaddada ingantattun ƙa’idojin karatu a BUK, wanda ta ce ba za ta lamunci satar jarrabawa ko laifuffuka makamantan haka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp