Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke akalla mutane 35 da ake zargi da laifin fashi da makami a wani samame da ta gudanar a cikin mako guda, wanda ya mamaye yankunan Ajah zuwa Elemoro.
Da yake tabbatar da kamen a ranar Asabar, mai magana da yawun ‘yansandan, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame na dabaru daban-daban a yankin Ajah.
- Nijeriya Ta Yi Asarar Tiriliyoyin Naira Kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba – Gwamnati
- NNPC Da Matatar Dangote Na Gasar Rage Farashin Fetur
Daga cikin wadanda aka kama a ranar 24 ga Fabrairu, akwai Alao Oluwafemi, Adeshina Akinrinde, Udoh John, Afolabi Kola, Daniel Augustine, Olalekan Kudus, Shittu Lanre, da Azeez Olalekan.
Sauran wadanda aka karba a cikin wannan mako sun hada da Olayemi Moses, Oriyomi Ojo, Ismail Mubarak, Alabi Ibrahim, Bashir Umar, Nasiru Muhammed, Ashiru Sanni, Babalola Ibrahim, John James, Rafiu Yakubu, da Basit Azeez.
A cikin jerin sunayen akwai Adebayo Oyebode, Oriyomi Williams, Sahabi Lawal, Benjamin Peter, Aanu Ayoade, Aminu Abubakar, Olayiwola James, Sahedu Abubakar, Taiwo Fawasi, Muhammed Monsuru, Abdullahi Ibrahim, Uche Achuoye, Samuel Olapade, El-Kamal Ibrahim, Hammed Taofeek, da Jamilu Usman.
Da yake magana kan aikin, Hundeyin ya bayyana cewa, kungiyoyi masu amfani da dabaru da ke Elemoro ne suka yi kamen, inda suka rufe hanyar Ajah, ciki har da Lekki Phase 1 zuwa Epe.
“Tawagarmu ta dabara da ke Elemoro ce ta gudanar da wannan aiki tare da rufe adis na Ajah, kamar Lekki Phase 1 zuwa Epe. Sun gudanar da wannan aiki.
Aanu Ayoade, Aminu Abubakar, Olayiwola James, Sahedu Abubakar, Taiwo Fawasi, Muhammed Monsuru, Abdullahi Ibrahim, Uche Achuoye, Samuel Olapade, El-Kamal Ibrahim, Hammed Taofeek, and Jamilu Usman.
“Muna da kungiyoyin dabaru a wasu sassan jihar, kuma suma suna da irin wannan na kama masu aikata laifuka tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.
Da aka tambayi CSP Hundeyin game da dabarun da suka biyo bayan yawaitar kama mutane a cikin kankanin lokaci da kuma yiwuwar tsawaita su zuwa sauran yankunan da ke fama da aikata laifuka a jihar, CSP Hundeyin ya mayar da martani, “Kowace tawaga mai dabara tana da hurumi iri daya.
A cikin jerin sunayen akwai Adebayo Oyebode, Oriyomi Williams, Sahabi Lawal, Benjamin Peter, Aanu Ayoade, Aminu Abubakar, Olayiwola James, Sahedu Abubakar, Taiwo Fawasi, Muhammed Monsuru, Abdullahi Ibrahim, Uche Achuoye, Samuel Olapade, El-Kamal Ibrahim, Hammed Taofeek, da Jamilu Usman.
Da yake magana kan aikin, Hundeyin ya bayyana cewa, kungiyoyin dabara da ke Elemoro ne suka yi kamen, inda suka rufe hanyar Ajah, ciki har da Lekki Phase 1 zuwa Epe.
PUNCH Online ta samu labarin cewa an gurfanar da dukkan mutanen 35 da ake zargin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp