A kwanakin baya ne aka tabbatar da mutuwar mutum 6 yayin da wasu dama suka ji raunuka a wani taho-mu-gama da jirgin kasa da motar ma’aikatan (BRT) ta yi a yankin Shogunle da ke Ikeja, a Jihar Legas.
Rahottani sun nuna cewa, motar na kokarin tsallake hanyar jirgin ne daidai lokacin da jigin ke shigowa inda jirgin ya yi karo da motar ya kuma tafi da ita daga tashar PWD har zuwa tashar Shogunle, tafiyar4 kusan nisan mita fiye da 100.
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
Idan kuma za a iya tunawa, a watan Disamba ne na shekarar da ta gabata jirgin kasa dauke da mutane da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi karo da motar wata mata inda anan take ta ce ga garinku nan, hatsarin ya faru ne a daidai unguwar Chikakore da ke yankin Kubwa a yankin babbar birnin tarayya Abuja.
Haka kuma a watan Janairu wani jirgin da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya kauce wa hanya a Abuja sai dai cikin ikon Allah babu wanda ya rasa ransa a hatsarin.
Ba zai yiwu mu manta a cikin sauri ba harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa a jihohin Kaduna da Edo ba a cikin watannin 12 da suka wuce, inda har aka kai ga rasa rayukanh mutane da dama, baya ga mutanen da aka yi garkuwa da su, lallai bai kamata irin wannan ya sake faruwa ba.
A ra’ayin wannan jaridar, aukuwar hatsarin da aka samu a na baya-bayan na a Jihar Legas da Abuja sun bayyana bukatar a yi maganin matsalar tare da daukar mataki na kawo karshen yawaitar hatsarin da ke tattare da sufurin jirgin kasan Nijeriya. A bayyana yake cewa, ana bukatar a tabbatar da daukar matakan da suka kamata don kare aukuwar ire-iren wannan hatsaruran a nan gaba.
Wadanna hatsuran suna kara fito da manyan matsalolin da bangaren sufurin jiragen kasan Nijeriya ke fuskanta ne, kuma da bukatar a gaggauta daukar matakin kawo karshen su.
Kafin wannan gwamnatin ta dauki matakin farfado da sashin sufurin jirgin kasa, bangaren ya yi fama da rashin kulawa na tsawon shekaru masu yawa daga gwamnatocin da suka gabata.
Domin ganin an kawo karshe ko rage hatsarin jingin kasa da ake samu a Nijeriya akwai bukatar masu ruwa da tsaki su gaggauta daukar matakin ganin an warware matsalolin da sashin ke fuskanta.
A ra’ayinmu akwai bukatar da a samar wa tsarin jirgin kasan Nijeriya cikkaken kayan aiki na zamani tare da daga darajar wadanda ake da su a halin yanzu. Dole gwamnati ta zuba manyan jari a kokarin samar da kayan aiki na zamani. Wannan ne zai tabbatar da jiragen za su iya yin gudu tare da kuma rage aukuwar hatsurar da ake samu a kai-kai.
Haka kuma yakamata a rika sanya tare da kula da kayyakin aiki. Ya kuma kamata gwamnati ta zuba jari wajen horar da ma’aikata don su samu sanin makaman aiki da sabbin na’urorin da ke shigo da su.
Muna kuma bayar da shawarar da a samar da wasu ka’idoji na tabbatar da kariya a harkar tafiyar da safarar jiragen kasa. Dole ne kuma hukumomi su tsayu don ganin ana aiki da dokokin da aka samar ta hanyar amfani da kwararrun ma’aikatan da ake da su.
Akwai kuma bukatar a inganta kafafen sadarwa a tsakanin direban jiragen da cibiyar da ke bayar da umarnin zirga-zirgan don kare aukuwar hatsari. Dole gwamnati ta zuba isashen jari a kayayyakin sadarwa na zamani ta yadda za a iya sanar da direban jirgi halin da hanyoyin dogo ke cik don kare aukuwar hatsari.
A wani bangaren kuma al’ummar Nijeriya da dama basu san ka’doji da alamomin hanyar jirigi ba saboda yadda aika yi watsi da bangaren na tsawon lokaci. Dole gwamnati ta farfado ta hanyar gangami na musamman na fadakar da al’umma a kan irin munin da ke tattare da hatsarin jirgin kasa.
Wannan zai tabbatar da cewa al’umma na sane da irin hatsarin da ke tare da tsallake hanyar jirgin kasa tare da kuma daukar matakin kariya da kuma bin dokokin da aka shimfida.
Bayan wadannan matakan da muka zayyana, akwai kuma bukatar gwamnati ta hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu don suma su zuba jari a harkar sufurin jirgn kasa. Shigo ga kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen bunkasa bangaren zai kuma kara inganta tsaro da yadda ake gudanar da bangaren gaba daya.
Ba tare da wani kokwanto ba, yawancin hatsarin da ake samu yana faruwa ne sakamakon sakaci na dan adam, kuma gashi har yanzu ba aji labarin an hukunta wani ko wata ba. Kamar yadda muka sha fada laifuka na cigaba da bunkasa a Nijeriya ne saboda ba a kai ga hukunta masu aikata laifin.
Hatsarin jirgin da ya auku na baya-baya nan a Legas da Abuja ya kamata su zama sun zaburar da gwamnatin tarayya da hukumar kula da jiragen kasa a Nijeriya a kan bukatar da samar da cikakken kulawa ga hanyoyin jiragen kasa.
Mun yi imanin cewa, inhar aka yi amfani da wadannan shawarwarin za a samu raguwar hatsarin jiragen kasa a Nijeriya.