ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Sanin Hakikanin Halin Da Tattalin Arzikin Nijeriya Ke Ciki

by Leadership Hausa
10 months ago
Arzikin

Masu iya magana suna cewa, Jumma’ar da za ta yi kyau,tun daga Laraba ake gane ta, wannan maganar,ta yi daidai, idan aka yi la’akari da yadda alkalumman yanayin tattalin arziki na 2024 suka nuna, ya kasance, inda hakan ya zama wata ‘yar manuniya ce kan yanayin da Nijeriya za ta kasance, a 2025.

Misali yadda a 2024 wanda ta gabata, matsin rayuwa ya janyo wasu talakawan kasar suka rasa rayukansu, a yayin da aka yi turmutsin rabon kayan tallafin abinci, hakan ne ya nuna a zahirin gaskiya, ko shakka babu lamarin ya kai makura.

  • Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
  • Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano

Cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya da ke kan mulki ta yi, da kuma karyewar darajar Naira,hakan ne ya kara janyo wata babbar barazana da kuma kara jefa talakawan Nijeriya, a cikin kangin talauci.

ADVERTISEMENT

Biyo bayan cire tallafin man, farashin kayan masarufi da yadda al’ummar kasar, ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum, sun kara hauhawa, tare da kuma janyo hauhawar farashin kaya da kara haifar da rashin ayyukan yi.

Kazalika ma,lamarin ya janyo wasu kamfanoni da dama da suke gudanar da ayyukansu,ko dai sun fice daga kasar, ko kuma sun garkame kamfanonin, musamman ma saboda karyewar darajar Naira da kuma tsadar gudanar da ayyukansu.

LABARAI MASU NASABA

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

Wannan kalubalen, ya janyo Nijeriya ta yi asarar dimbin kamfanonin da suka zuba jarinsu a kasar wanda ya kai na yawan biliyoyin dala.

Bugu da kari kuma, sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta kirkiro da su, alamu ne da suke nuna cewa, ana samun jinkiri wajen kokarin da gwamnatin ke yi, na cike gibin, duk da kokarin da ake yi, na samo masu zuba hannun jari na kai tsaye, daga ketare.

Misali, wani fitaccen kamfanin hada magunguna na kasa da kasa wato GladoSmithKline, a watan Agusta ne 2023 ne, ya bayyana dakatar da gudanar da ayyukansa, a Nijeriya.

Wannan lamarin ya nuna cewa, sai dai Nijeriya ta koma shigo da magunguna daga ketare, inda kuma za ta rinka kashe dimbin kudade,wajen shigo da magungunan da kamfanin ke sarrafawa zuwa cikin kasar.

Kasancewar Nijeriya na kan matakin da ‘yan kasar ba wuya sun kamu da rashin lafiya, musamman  ma saboda karancin abinci mai gina jiki, lamarin da zai iya kara munana.

Kazalika ma, kamfanin P&G, shi ma ya tattara kayansa ya bar kasar, saboda kalubalen samun Dalar Amurka a Nijeriya.

A farkon watanni shida na 2024, sama da kamfanoni biyar ne suka fice daga Nijeriya, saboda rashin samar da kyakkyawan yanayin yin kasuwanci.

Kamfanonin su ne; Microsoft, Total Energies,PZ Cussons Nigeria Plc da dai sauransu, inda suka koma wasu kasashe da ke makwabtaka da Nijeriya, da suke da kyakkyawan yanayi na yin kasuwanci.

Ficewar wadannan kamfanonin, yana kara nuna yadda darajar Naira ta kai ga munzalin karyewar darajar ta wanda kuma hakan zai janyo nakasu ga bangaren zuba hannun jari a kasar.

Hakazalika, a wani rahoton kwanan baya da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar, ya nuna yadda hauhawar farashin kaya, a watan Nuwambar 2024, a kasa ya kai matakin kashi 34.6.

Haka hauhawar farashin kayan abinci, ya kai kashi 40, inda hakan ya kara jefa talakawan Nijeriya, a cikin kangin talauci.

A cewar alkalumman Hukumar Kula da Farashin Kaya ta kasa CPI rahoton Hukumar kula da harkokin kididdiga ta kasa ya nuna cewa, lamarin ya ci gaba da karuwa ne har zuwa sama da watanni uku, inda a watan Nuwamba ya karu da da kashi 0.72, idan aka kwatanta da yadda na watan Okutobar 2024 yake.

Kazalika, wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar da ya nuna  yadda sama da ‘yan Nijeriya miliyan 14, suka fada a cikin kangin talauci a cikin watanni 18.

Lamarin abin takaici ne la’akari da yadda ‘yan Nijeriya sama da miliayn 133 a  shekarar 2024, suke ci gaba da fuskantar talauci.

Domin a lalubo da mafita kan wannan kalubalen, gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudi ga majalisar kasar na Naira tiriliyan 47.9.

Sai dai kuma, ta hanyar kasafin kudin, gwamnatin Tinubu, ta ayyana nufin samar da sauki kan abubuwan da aka fi bukata na yau da kullum,ciki har da rage yawan hauhawar farashin kaya daga kashi 34.6, zuwa kashi 15, tare da farfado da darajar Naira akalla daga Naira 1,700 zuwa kan duk Dala daya 1,500.

Sai dai, akwai gibin da ya kai  sama da Naira tiriliyan 13 a cikin kasafin kudin, wanda hakan ne,ya ke haifar da fargaba,dalilin hakan ne ya sa dole ne gwamnatin, ta ciwo bashi, domin ta cike gibin a cikin kasafin kudin.

Kamar yadda wannan Jaridar ta ruwaito a ranar 30 ga watan Disambar 2024, masu fashin baki da kwararru a fannin tattalin arziki, suna da yakin cewa,idan aka farfado da darajar Naira aka rage farashin man fetur a 2025, aka kara karfafa samar da kudaden musaya na waje, da kuma rage shigo mai,za a samu sauki.

Wannan yakinin na su, ya zo daidai da ake kara samar da mai a kasar ta hayar sarrafa shi a cikin kasar, wanda hakan zai samar da sauki a kan kudin kasar.

Kazalika ma, wannan samun ci gaban da aka samar, zai daidai ta, farashin mai.

A sakonsa na sabuwar shekarar 2025, Shugaba Tinubu ya mayar da hankali ne, kan rage hauhawar farashi daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 a karshen 2025.

Sai dai kuma,furucin na sa ya nuna aukwar lamarin a zahiri, idan aka yi la’akari da yadda tattalin arzikin kasar, ke ci gaba da fuskantar kalubale.

Kasafin kudin na Naira tiriliyan 47.9 na tare da gibin da ya kai na sama da Naira tirliyan 13, wanda hakan ya sa manyan tamboyi, fiye da bayar da amsa, game da daburun da gwamnatin za tayi amfani da su.

Yakinin gwamnatin game da daga darajar Naira daga Naira 1,700 a kan duk dala daya 1,500, hakan ya nuna ana sa rai na samun karuwa a musayar kudaden  waje da kuma rage shigo da shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno
Manyan Labarai

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

November 18, 2025
Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

November 17, 2025
Next Post
Ministan Labarai

Ba Mu Buƙatar Amincewar Sanusi Kan Tsare-tsarenmu Na Tattalin Arziki - Minista

LABARAI MASU NASABA

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

November 18, 2025
Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.