Dan wasan gefe na Arsenal, Bukayo Saka ya nemi afuwar magoya bayansa da kungiyarsa bayan zubar da bugun fanariti da ya yi a wasansu da West Ham a ranar Lahadi.
Saka ya samu damar da zai maida wasan ya kasance da ci 3-1 a rabin farko na karawar da kungiyarsa ta yi da West Ham a filin wasa na Landan, amma ya jefa kwallon waje a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Arsenal ta samu maki daya bayan tashi kunnan doki 2-2 a wasan wanda hakan ya bai wa abokiyar hamayyarta Manchester City kwarin guiwa a fafatawar neman kofin.
Bayan tashi wasan, Saka ya nemi afuwar magoya bayan Arsenal a shafinsa na sada zumunta na Instagram.
“Duk yadda sakamakon wasan ya kasance, a koyaushe zan karbi kuskurena. Ina neman afuwar magoya bayanmu, zan yi duk abin da zan iya don gyara kuskure da samun nasara a wasannin gaba” in ji shi a Instagram.
Yanzu dai Arsenal ce ke jagorantar Man City da maki hudu kacal a teburin gasar ta Firimiya.
Arsenal tana da maki 74, ta buga wasannin 31. Manchester City tana da maki 70, ta buga wasanni 30.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp