Gwamna Dauda Lawal ya taya daukacin al’ummar Musulmin Zamfara da Nijeriya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
A ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ce aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) wacce ta yi dai-dai da ranar 27 ga watan Satumba, 2023.
- Bukukuwan Maulidi: Ministan Abuja Ya Taya Mazauna Birnin Murna
- Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
Mataimaki na musamman a bangaren yada labarai na gwamna Dauda, Suleman Bala Idiris ne ya bayyana hakan a takardar da ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a ranar Laraba.
Acewar sa, Gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi da su rika girmama watan Mauludin kuma su dinga dabi’antuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) ta juriya, taimakon juna da hakuri.
Ya kara da cewa, Gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara da Kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp