Bayan da gwamnatin kasar Sin ta nuna sakamakon kidayar tattalin arzikin kasa karo na 5 a kwanan nan, kafofin watsa labaru na kasashen waje da dama sun yaba da sakamakon matuka.
Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a shekarar 2023, kasar Sin ita ce ta biyu a duniya a karfin tattalin arziki. Cikin shekaru biyar da suka wuce, yawan gudummawar da Sin ta bayar wajen habakar tattalin arzikin duniya ya kai kusan kashi 30 cikin dari, wanda ya sa ta zama tushen ci gaban tattalin arzikin duniya mafi girma.
Tare da zurfafa aiwatar da shirin raya kasa ta kirkire-kirkire, an samu nasarori masu dimbin yawa a kasar Sin. Ya zuwa karshen shekarar 2023, yawan manyan kamfanonin kasar Sin da suka samun saurin ci gaba sun kai 158,000, wanda ya kai fiye da kashi daya bisa biyar na dukkan manyan masana’antu da harkokin ba da hidimomi.
Dangane da samun ci gaba mai dorewa kuwa, yawan motoci dake amfani da sabbin makamashi da kasar Sin ta samar ya kai miliyan 9.458 a bara, adadin da ya ninka 6.9 a kan shekarar 2018, kuma ya zama na farko a duniya tsawon shekaru tara a jere, wanda ya kai sama da kashi 60 cikin dari na jimillar ta duniya baki daya.
A cikin shekaru biyar da suka gabata, yanayin kasa da kasa ya sami sauye-sauye masu zurfi da sarkakiya. Yayin da ake fuskantar kalubale daban-daban, tattalin arzikin kasar Sin ya nuna matukar juriya. A cikin wannan lokaci, masana’antar kera kayayyaki ta kasar Sin ta farfado cikin sauri, kuma ta samar da karin kayayyaki, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki na duniya yadda ya kamata, haka kuma ta ba da babbar gudummawa wajen ci gaban tattalin arzikin duniya. (Safiyah Ma)