Tsohon hafsan hafsan sojin Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya jajirce wajen ganin Nijeriya ta samu ‘yancin cin gashin kai tare da nuna goyon baya ga shawarar Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu kin bari sojojin kasashen waje su kafa sansani a qasar nan.
Bayanin Buratai ya biyo bayan zargin da wasu shugabannin Arewa suka yi a baya-bayan nan na cewa gwamnatocin Amurka da Faransa na neman Nijeriya ta rattaba hannu kan wasu sabbin yarjejeniyoyin tsaro, tare da share hanyar sake tsugunar da sojojin da aka kora daga yankin Sahel.
- An Fara Bincike Kan Yadda Jami’in Kwastam Ya Kashe Kansa A Kano
- Sanata Hanga Ya Kare Sukar Da Ake Yi Masa Kan Tallafin Tukwanen Yumɓu Da Likafani
“Bai kamata Nijeriya ta kyale duk wasu sojojin kasashen waje su kafa sansani a kasarta ba. Ina yaba wa gwamnatin tarayya bisa matakin da ta dauka na karbar sojojin Amurka da ake shirin janyewa daga jamhuriyar Nijar zuwa Nijeriya,” in ji shi a tattaunawar da ya yi jaridar THISDAY.
Ya kara da cewa, “Mai girma ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ya bayyana karara cewa Nijeriya ba ta da wani shiri na tsugunar da sojojin Amurka a kasarmu.”
A wata wasika da suka aike wa shugaba Tinubu kwanan nan, wasu daga cikin shugabannin arewa sun yi gargadin cewa kasancewar sansanonin sojan kasashen waje zai kara dagula dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da jamhuriyar Nijar da ma makwaftaka da kasar Faransa, inda suka roki shugaban da ya ba da fifiko kan tsaron kasa.