Shekarar da ta gabata ta kasance shekarar da ‘yan Nijeriya ba za su taba mantawa ba. Shekarar 2023 ta zo yayin gabatowar babban zaben kasa ta kuma kammalu ne da harin ta’addancin nan da aka kai a ranar kirsimeti a Jihar Filato.
A daidai lokacin da aka fuskanci matsanancin matsalar tattalin arziki sakamakon shigowar sabuwar gwamnatin shugaban Kasa Bola Tinubu, hakan kuma ya bude kofar tsananta matsalar da al’ummar Nieriya suka ci gaba da fuskanta a cikin shekarar duk kuwa da yekuwar sabunta kwarin gwiwa da gwamnatin take yi wa ‘Yan Nijeriya.
Amma kuma duk da wadannan matsalolin, a wannan shekarar ta 2024 akwai wasu abubuwa da ‘yan Nijeriya ke da burin samu in har ana son su kara samun tabbacin cewa, fatan da suke yi na samun rayuwa mai inganci a Nijeriya a nan gaba ba zai tafi a banza ba.
Na farko shi ne sake fasalin tsari da dokokin zabe da kuma bukatar samar wa bangaren shari’a gurbi a tsarin harkokin siyasar kasar nan. Abubuwan da suka faru a babban zaben 2023 da kuma yadda aka tafiyar da kararrakin zaben a kotuna sun zama abin kunya.
Fafutukar wasu ‘yan Nijeriya da dama da kuma kungiyoyi masu zaman kansu tana bukatar a samar da doka da za ta amince da aikawa da sakamakon zabe daga akwatunan zabe zuwa babbar tashar tattara sakamakon zabe ta INEC don a kauce wa magudin zabe bai kai gaci ba, saboda yadda aka lankwasa dokar ta yadda aka ba INEC damar yin yadda ta gama wajen aikawa da sakamakon zabe.
Yadda INEC ta gudanar da zaben 2023 ya sanya al’umma ke kira tare da bukatar a kara karfafa dokokin zabe ta yadda zai zama dole ta tantance masu kada kuri’a tare da tabbatar da aikawa da sakamakon zabe ta intanet a zabuka masu zuwa a nan gaba.
Haka kuma a karon farko a Nijeriya, zaben 2023 ya samar da shugaban kasa mai karancin kuri’u. Shugaba Bola Tinubu ya samu nasarar lashe kashi daya bisa uku ne na kuriu’un da aka kada a zaben shugaban kasan da aka yi.
Ya kamata a samar da dokar zaben da za ta samar da wanda ya lashe zabe a zabukan shugaban kasa da na Gwamna ko kuma shugaban karamar hukumar da kuri’un da aka kada akalla da kashi 50 a cikin dari a karon faro ko kuma a zagaye na biyu.
Wasu abubuwan da aka gabatar a yayin sauraron kararrakin zabukan zaben sun kara nuna bukatar a samar da karin canje-canje a dokokin zabe. ‘Yan Nijeriya za su so ganin an wawarware dukkan rikice-rikice da suka taso sakamakon zabukan fidda gwani kafin a gudanar da zabe da kuma ganin an warware dukkan matsalolin da suka taso sakamakon zabukan da aka gudanar kafin a rantsar da wadanda suka samu nasara.
Bayan kasancewa shari’un suna katsalanda ga harkokin gudanar da mulki suna kuma kara wa wanda ake kalubalantar nasararsa karfi a shari’un da ake yi.
Wadanda aka rantsar suna iya amfani da karfin kujerar da suke a kai wajen tabbatar da nasara ga kansu.
‘Yan Nijeriya na kuma bukatar ganin hukumar zabe mai zaman kanta tun daga yadda ake nada manyan jami’anta don kada a fada wa tarkon ‘yan siyasa.
Haka kuma bai kamata a ce, wasu masu shari’a ‘yan kalilan ne suke da hurumin yanke hukuncin wanda ya yi nasara a zabukan da aka gudanar ba.
A wannan tsarin na yanzu an dora wa wasu mashari’a nauyi, wasu kuma daga cikinsu za su iya aikata son rai in har suka samu abin da suke so. Kamar yadda lamarin ke ta kara karuwa, ana iya watsi da kuri’un da al’umma suka kada saboda wasu kalkale-kalkalen shari’a a kotuna.
In har wani mashari’a ya gano wata matsala a zaben da aka yi to ya kamata ne ya umarci a koma wajen al’umma don sake dauko ra’ayoyin al’umma. Dukkan wadanna na bukatar a sake yi wa dokokin zabe kwaskwarima.
Rashin tsaron rayuka da dukiyar al’umma na daga cikin abubuwan da ‘Yan Nijeriya ke fata a kawo karshe a 2024. A wannan kasar da yawa daga cikin masu aikata laifi suna watayawa ba tare da an hukunta su ba.
‘Yan Nijeriya na bukatar ganin jami’an tsaron da za su gano tare da kawo kawo karshen masu aikata laifukka tun daga kananan barayi, manyan ‘yan damfara, ‘yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.
Suna fatan ganin jami’an tsaron da za su yi aiki ta hanyar amfani da bayanan sirri da kuma kayan aiki na zamani ba kamar yadda abin yake a halin yanzu ba, in ba haka to maganar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III na cewa, a kullum ‘yan ta’adda na riga jami’an tsaromu shiri zai kasance gaskiya kenan.
Yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kauyuka 20 a cikin kwanaki 2 a Jihar Filato ba tare da samun wata turjiya ba daga jami’an tsaromu abu ne da bai kamata a amince da shi ba, ya kamata a tabbatar da an hukunta wani ko wasu da ke da alhakin wannan sakacin in har ana son a dauki gwamnati da muhimmanci.
A kan tattalin arziki, ‘Yan Nijeriya na bukatar ganin an rage musu nauyin matsalar tattalin arzikin da suke fuskanta. Yadda ake samun hauhawar farashin kayayyakin masarufi musamman kayan abinci da ya tashi da kashi 32.8 (a kididdigar da aka yi a ranar 15 ga wata Disamba 2023), yana kara tura al’umma ne zuwa kangin talauci inda fiye da kashi 63 daga cikin al’umma Nijeriya miliyan 133 da aka kiyasta a shekara a 2021 suna cikin kangin talauci.
‘Yan Nijeriya na bukatar gwamnati ta samar da hanyoyin kawo karshen matsalolin tsaro da sassan kasar ke fuskanta.
Haka kuma ‘Yan Nijeriya na bukatar jami’an gwamnati su zama abin misali wajen tafi da harkokinsu, ba zai yiwu su rinka yekuwar al’umma su ci gaba da sadakarwa ba alhali su kuma suna rayuwar bushasha suna kashe kudaden gwamnati ba tare da tausayawa ba.
‘Yan Nijeriya na bukatar gwamanati ta kawo karshen yadda take cin bashi tare da kuma ganin an yi amfani da basukan da aka ciwo ta hanyar da ta kamata.
A halin yanzu Nijeriya na amfani na kashi 95 na kudaden shigarta wajen biyan bashin da ake bin ta. Maimaikon cin bashi, ya kamata Nijeriya ta toshe ayyukan cin hanci da rashawa musamman a ma’aikatu da hukumomin gwamnati musamman ta hanyar aringizon kudaden kwangila da tafiye-tafiye kasashen waje.
Daga karshe ‘yan Nijeriya na bukatar ganin an rungumi akidar nan ta rarraba iko a tsakanin bangarorin gwamnati, yadda aka ba gwamnatin tarayya karfi fiye da kima yana kawo cikas ga ayuyykan yaki da matsalar tsaro da kuma bunkasar yankunan karkara. A matsayinmu na gidan jarida muna yi wa ‘Yan Nijeriya fatan alhairi a shekarar a 2024.