Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yaba wa ayyukan majalisar ta 10, inda ya ce a cikin watanni 6 shida na farko tun bayan kaddamar da majalisar a ranar 13 ga watan Yunin 2003, sun amince da kudurori 120.
Ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wurin zaman hutu na majalisar wakilai da ya gudana ranar Asabar.
- Yadda ANA Ta Shugabanci Gangamin Saukaka Zuwa Hajjin 2024 A Nijeriya
- Kasashen Afirka Na Fadada Cudanya Da Kasar Sin A Fannoni Daban Daban
Haka kuma Abbas ya yaba wa abokan aikinsa bisa yadda suka nuna kwarewa da kuzari a cikin watanni shida da suka gabata.
“Sakamakon da muka samu a zauren majalisar wakilai a cikin watanni shida da suka gabata na da ban mamaki. Majalisar ta samu gabatar da kudurori 962 da muhawara 500 da kuma korafe-korafe 153.
“A cikin wadannan kudurori 120 sun tsallake karatu na biyu. A halin yanzu ana ci gaba da bita da kuma gyare-gyare don magance wasu matsalolin da aka taso da su yayin muhawarar,” inji shi.
Ya kuma kara da cewa an mika wasu kudirori 120 ga kwamitoci domin yin nazari mai zurfi a kai.
A cewarsa, “Mun samu nasarar zartar da wasu kudirori da dama wadanda aka mika wa majalisar dattawa domin su yi aiki a kai.
“A cikin wadannan kudurorin akwai dokar lantarki da ka yi wa kwaskwarima ta 2023 da dokar binciken ma’aikatar tarayya da aka yi wa gyara ta 2023 da dokar kayyade kudade ta 2023 da aka yi wa gyaran fuska da dokar rantsuwa ta 2023.
“Sauran wasu muhimman kudirori da majalisar ta zartar sun hada da dokar hana haduwar kananan makamai da ta 2023, dokar hukumar kashe gobara ta tarayya ta 2023, dokar gudanar da shari’a kan manyan laifuka ta 2023, dokar hukumar raya yankin Neja Delta, kudirin dokar kafa majalisar binciken likitocin Nijeriya ta 2023, dokar kafa hukumar samar da zaman lafiya ta Nijeriya ta 2023 da kuma dokar kafa hukumar raya yankin kudu maso gabas ta 2023.