Majalisar wakilan jama’ar Sin ta saurari sakamakon bincike kan rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin na shekarar 2025 a jiya Laraba, lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa.
Abin da aka fi zura ido shi ne burin da gwamnatin Sin ta saka gaba na samun bunkasar karin tattalin arzikinta, watau GDPn kasar a bana da kashi 5%.
- Idan Kunne Ya Ji, Jiki Ya Tsira
- Sin Za Ta Kara Ingiza Samar Da Kudaden Gudanar Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu
Wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa sun ba da labarin cewa, abin ya dace da hasashen da aka yi mata, kuma adadin ya yi daidai da na shekaru biyu da suka gabata, wanda ya bayyana niyyar gwamantin ta ba da tabbaci ga samar da isassun guraben ayyukan yi da kyautata zaman rayuwar jama’a, a wani bangare na daban kuma, ya biya bukatun samun bunkasa na matsakaici da dogon lokaci.
Ma’anar samun bunkasar GDPn kasar da kashi 5% na kara bayyana a cikin ayyukan dake da nasaba da gaggauta samun ingantattun dimbin ci gaba da Sin take kokarin cimmawa.
Bari mu duba manyan ayyuka 10 da gwamnatin Sin ta girka a bana, abin da aka sa gaba ba shakka shi ne gaggauta sayayya da cin moriyar zuba jari da habaka bukatun cikin gida daga mabambantan bangarori. Daga cikinsu abu mafi bayyana muhimmanci wajen habaka bukatun cikin gida da inganta ciniki cikin gida shi ne gaggauta sayayya.
Ban da wannan kuma, muhimmancin wannan adadi na bayyana a bangaren iyawa da hazikanci na dan Adam. Rahoton ayyukan gwamnati na bana ya ambaci wannan abu sau da dama, ciki har da yawan amfani da na’urori dake iya sarrafa dimbin bayanai da hazikancin koyo mai zurfi da daidaita dimbin ayyuka masu sarkakiya, da kuma iyakacin kokarin bunkasa kera motocin sabbin makamashi masu aiki da basirar dan Adam. Kazalika da wayoyin salula da kumfuta da mutum-mutumin inji a wannan bangare.
Wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa na ganin cewa, bunkasar wannan fanni da Sin take samu za ta yi kwaskwarima kan yanayin kirkire-kirkire a sana’o’i daban-daban na duniya, kuma kasashen duniya za su more karin ci gaba da Sin take samu ta fuskar kimiyya da fasaha na zamani. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp