Saudi Arabiya na gab da samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2034 bayan Australia a hukumance ta sanar da janyewa daga shirin.
Tun da farko dai FIFA ta yanke shawarar yin la’akari da tayin kasashen Asiya da Oceania ne kawai na gasar ta 2034.
- Kotu Ta Yanke Wa ‘Yan Daudu 8 Hukuncin Daurin Watanni 3 A Kano
- Hukumar ‘Yansanda Ta Tabbatar Egbetokun A Matsayin Sufeto-Janar Na ‘Yansanda
A halin da ake ciki kasar Australia a ranar Talata ta bayyana daukar matakin janyewa daga yunkurin daukar nauyin gasar.
Ta ce ta mayar da hankalinta wajen karbar bakuncin gasar cin kofin Asiya ta mata ta AFC a shekarar 2026 da kuma gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa a shekarar 2029.
Kasashen da ke da sha’awar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2034 an ba su wa’adin ranar 31 ga watan Oktoba, tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga gasar kafin ranar 30 ga watan Nuwamba.
Kasar Saudiyya dai ta zuba jari mai yawa a fagen bunkasa kwallon kafa abin da ya bunkasa gasar ‘Pro League’ ta kasar wadda ta samu tagomashi na fitattun ‘yan wasan Turai ciki har da Cristiano Ronaldo da ya zo a shekarar da ta gabata.
Sama da mambobi 70 na FIFA sun fito fili sun goyi bayan yunkurin Saudiyya, kuma Sheikh Salman na Bahrain, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Asiya, ya amince da shirin.