ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burin Sin Na Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Bai Sauya Ba

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Yanzu haka dai hankalin duniya ya karkata ne ga rikicin dake faruwa tsakanin Palasdinu da Isra’ila, inda duk wayewar gari rayuka ke salwanta tsakanin bangarorin biyu.

Kuma tun kafin ta zama shugabar karba-karba ta kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ke ta kira tare da gabatar da matakai a lokuta daban-daban, na kawo karshen tashe-tashen hankulan dake faruwa a sassan duniya. Sannan bayan da ta karbi shugabancin karba-karba na kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ta jaddada kudurinta na ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa, wajen sa kaimi ga kwamitin sulhu na MDD na daukar matakan da suka dace na tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki, da rage yanayin jin kai da ake ciki, da taka rawar da ta dace wajen samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Isra’ila ta hanyar “shirin kafa kasashe biyu”.

  • Darajar Cinikayyar Kasar Sin A Ketare Ya Karu Da Kaso 0.03% Cikin Watanni 10 Na Bana
  • Kwamishinan Cinikayya Da Zuba Jari Na Najeriya Dake Shanghai Ya Yaba Da Manufofin Kasar Sin Na Fadada Bude Kofa Ga Kasashen Waje

Sin na kara bayyana cewa, wajibi ne kasashen duniya su dauki matakin gaggawa, kuma kasashen dake wajen yankin, musamman ma manyan kasashe, su tabbatar da gaskiya da adalci, tare da taka rawa mai ma’ana wajen ganin an sassauta yanayin da ake ciki.

ADVERTISEMENT

Idan ba a manta a ranar 1 ga watan Nuwamba, lokacin da kasar Sin ta karbi wannan shugabanci, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, halin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila shi ne batu mafi muhimmanci a ajandar kwamitin sulhu na wannan wata. Kana aikin dake kan gaba shi ne karfafa maganar tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin, da hana karin asarar rayukan fararen hula, bala’un jin kai, da rikice-rikice.

Kamar kullum Sin na Allah wadai da duk wasu matakai na muzgunawa, da kaiwa fararen hula hare-hare, domin rayukan al’umma na da matukar alfarma, kuma bai dace tashin hankalin da ake fama da shi ya haifar da salwantar rayukan fararen hula Falasdinawa ko Isra’ilawa ba.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Sin mai kaunar zaman lafiya na kira da a gaggauta komawa teburin shawarwari, domin kaiwa ga cimma matsaya, dangane da aiwatar da manufar nan ta warware riciki ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a kuma shata matakai daki-daki na cimma nasarar hakan.

Kuma a matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na majalisar na wannan karo, kasar Sin za ta yi biyayya ga kiraye-kirayen kasashen duniya, da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa, wajen sa kaimi ga kwamitin don daukar matakai na bai daya masu ma’ana cikin lokaci.

Wannan ya kara nunawa duniya cewa, kasar Sin tun fil-azal, kasa ce mai kaunar zaman lafiya ba neman tashin hankali ba. Sabanin wasu kasashe dake amfani da matsayi ko ikonsu na kara rura wutar fitina, ba tare da la’akari da rayukan dake salwanta ba. Domin zaman lafiya ya fi zama dan Sarki. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Daga Birnin Sin

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
Next Post
Gwamnatin Kaduna Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Kudancin Jihar Da Suka Bar Matsugunansu

Gwamnatin Kaduna Za Ta Sake Tsugunar Da 'Yan Kudancin Jihar Da Suka Bar Matsugunansu

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

November 12, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025
Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

November 12, 2025
Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

November 12, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.