Shugaban Kamfanin shirya fina-finan Hausa na ‘Nagudu Inbestment’ cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. Kana babban Marubucin fina-finan Hausa da ya shafe tsahon shekaru 25 cikin masana’antar ta Kannywood, Mustapha Shariff Anwar wanda aka fi sani da Sharu Nagudu, ya bayyana wa masu karatu irin namijin kokarin da suka yi wajen ganin sun gina kamfanin ‘Nagudu Inbestment’ tun a 25 da suka gabata. Haka zalika shugaban kamfanin ya bayyana kadan daga cikin bambance-bambancen da ke tsakanin fina-finan baya da na yanzu. Bugu da kari shugaban kamfanin ya yi karin haske tare da bada shawarwari ga masu kokarin shiga kamfanin har da wadanda suke cikin masana’antar Kannywood, da ma wasu batutuwa masu yawa, inda a ciki ya bayyana cewa, Burinsa harkar fim ta zama sana’a a Nijeriya kamar yadda ta ke a Indiya da Amurka. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA Kamar haka;
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi.
Sunana Mustapha Shariff Anwar, wanda aka fi sani da Sharu Nagudu.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a unguwar Bakin Ruwa, Karamar Hukumar Dala, a Jihar Kano, ranar 1-12-1964. Na yi makarantu da dama tun daga firamare har zuwa matakin Jami’ar Maryam Abacha, inda na yi digirin farko a fannin Lissafi, ‘Bsc Accounting’. Kuma ni ne mai kamfanin shirya fina-finai na ‘Nagudu Inbestment Limited Kano’.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Gaskiya na tsunduma masana’antar Kannywood ne domin ina da sha’awar raya al’adunmu na Bahaushe, kuma ina jin dadin na ga ana fadakarwa, musamman ta hanyar fina-finanmu na Hausa domin kafar talabijin ita ce kafa mafi saukin fadakarwa.
Za ka yi kamar shekara nawa da shiga cikin masana’antar?
Mun kafa kamfaninmu na ‘Nagudu Inbestment’ tun shekarar 1998, a kalla shekara 25 kenan, tun lokacin nake cikin wannan masana’anta.
A Matsayinka na shugaban kamfanin shirya fina-finan Hausa, shin ka taba sha’awar fitowa a fim ko ka sha fitowa matsayin Jarumi, ko kuwa tun daga wancan lokacin matsayinka na shugaban kamfani kake?
Gaskiya ni akan kaina ban taba fitowa a fim ba. Lokacin da na fada miki mun kafa kamfaninmu tare da Kawuna Faruk Nagudu shi ne Shugaba, a lokacin ni kuma ina yi masa Sakatare, a bayan rasuwarsa na zama Shugaba. Shi yana fitowa a fim, ni kuma ni ne tare da Khalil Germany da Abdul’aziz Madakin Gini muke rubuta duk fina-finan da kamfanin zai yi, har ma da na wasu kamfaninnika.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance a wancen lokacin?
To gaskiya ni ban samu wata matsala ba ko damuwa, domin wata hikima muka yi ni da kawuna Marigayi Faruk Nagudu wanda Allah ya yi wa rasuwa shekara tara da suka gabata. A lokacin mun je kafa da kafa har kamfanin Alhaji Hamisu Iyantama, muka sanar da shi muradinmu na kafa kamfani, da kuma shiga tsundum harkar fina-finai. Shi ne mutumin da ya bamu shawarwarin da muka bi har muka kafa kamfaninmu ba tare da wata matsala ba, shi ya sa ma muke kiran Iyantaman a matsayin uba ga ‘Nagudu Inbestment’.
Lokacin da za ka shiga cikin masana’antar, shin ka fuskanci wani kalubale daga wajen iyaye?
Alhamdulillah! A nan ma ban samu matsala ba, musamman da yake na fito daga gidan Malamai. Iyayena da kakannina duk Malamai ne, sa’annan yayye da Kawunni kuma duk ‘yan boko ne, kuma bokon gaske ba muna boko ba, don haka gidanmu duka akwai fahimta da wayewa.
Wanne irin kalubale kuka fuskanta bayan bude kamfanin?
Ai wannan lokacin dan fim kamar waliyyi ake kallonsa. Mutane har sha’awarka ake yi idan kana harkar fim. Saboda a lokacin abubuwan ba su tabarbare ba kamar yanzu. Akwai tarbiyya, mutumci da mutumtawa. Kamfaninmu ya karbu sosai a Arewacin kasar nan, domin daga garuruwa da yawa mutane sun barko zuwa kamfaninmu kasancewar ba fim kadai muke yi ba, har da harkar kida da waka. Ba na mantawa a lokacin mun kusan binne duk wani kamfani a Jihar Kano. Ina tabbatar miki da cewar duk wani mawaki da makidi wadanda suka amsa sunayensu duk sai da suka tare a kamfaninmu har suka zama ‘yan kamfani.
A cikin mawaka da ‘yan fim akwai masu lakabi da sunan Nagudu, shin su ma ‘ya’ya ne ga kamfanin ko kuwa suna ne ya zo daya?
To, Nagudu dai daya ne a Kano, wato Kakanmu kenan Marigayi Alhaji Abdullahi Nagudu. Don haka duk wanda kika ji yana lakabi da Nagudu shi yake nufi, ko da ya san kamfaninmu ko bai sani ba, ko ya yi aiki da mu ko bai yi ba, ko dan kamfaninmu ne ko ba dan kamfanin bane. Da yawa yaranmu ne masu lakabi da sunan, wasu kuma yaran yaranmu ne, wasu kuma cin arziki suke yi, dukkanninsu muna gode musu.
Wanne irin kalubale ka taba fuskanta a gaba daya shekarun da ka shafe cikin masana’antar?
To, ba zan ce miki ni ko mu mun taba samun kalubale ba musamman a Kamfaninmu ba, kasancewar mu masu bin doka ne matuka. Duk tsanani ko wahala ba ma yarda mu ko wani dan Kamfaninmu ya karya doka ba. Amma kuma zai yi wahala a share wadannan shekaru ba a samu wani cikas ba, don haka ina alakanta matsalar da ma’aikatar ta fuskanta lokacin Gwamna Shekarau da matsalar da ni da duk dan Kannywood muka samu, wanda ba ma fatan sake afkuwar irin wannan matsala a nan gaba.
Wanne irin nasarori kuka samu game da kamfaninku?
Ma sha Allah! Mun kasa kaya an saya, an kasa kaya mun saya, an kasa da sunanmu an sayar, ina fatan kin fahimta.
Har yanzu kamfanin na ci gaba kamar yadda yake a baya, ko kuwa ya dakata a yanzu?
Har yanzu kamfanin yana nan kuma dukkannin harkokinmu babu wanda muka fasa.
Idan mutum yana son shiga kamfaninku wanne mataki zai bi domin ya samu damar shiga?
Wannan tambayar ina jin dadinta a duk lokacin da aka yi min ita. Wajibi ne ga mai sha’awar shiga kamfaninmu mace ko namiji sai ya zo kamfanin mun yi masa tambayoyi, idan muka gamsu da bayanansa sai mu bashi ‘form’ ya cike. A cikin ‘form’ din akwai inda Mahaifi ko Mahaifiya ko wani Shakikin mutum zai sa masa hannu tare da lambar wayarsa. Za mu kira lambar mutumin mu tabbatar da abin da ya fada, idan mun gamsu za mu gayyato shi ko mu tura masa wakili domin mu samu yakini, kuma ko ba a garin nan yake ba muna tashin mutum ya je ya yi mana bincike musamman ma akan mata.
Idan na fahimce ka kamar kana magana ne akan sabbin dauka masu yunkurin shiga harkar, ko kuwa kuna daukar iya wadanda suke cikin masana’antar Kannywood bangaren waka da fim ne?
Wadanda suke cikin harkar ai babu bukatar bin wadannan tsauraran matakan kasancewar su dama ana tare, sabbi ne dama muke magana a kansu.
Me kake son cimma game da masana’antar?
Bukatata ba ta fice irin abubuwan da muka yi ba tun a baya, wato na sama wa matasa abin yi domin su ci gaba da dogaro da kawunansu ba. Sai kuma irin albarkar da mutanen gari suke sanya mana dangane da yadda suke amfana da fadakarwarmu.
Wanne mutum ne ke burge ka cikin masana’antar wanda ya zamo allon kwaikwayonka, da har kake ji da ma ka zamo tamkar shi?
Ado Ahmad Gidan Dabino.
Wadanne abubuwa ke ja hankalinka har kake jin da ma ka zama kamar shi?
Da farko dai ni da rubutu na fara a Kannywood, kin ga kuma shi ne baban marubuta, domin kaso casa’in na marubutan Kannywood da Littafan Hausa muna amfana da shawarwarinsa. Abu na biyu kuma shi dattijo ne mai dattako, wato dattijon da ya dattijantu. Abu na uku kuma shi adalin shugaba ne, mai sulhu a koda yaushe. Abu na hudu kuma yana da gaskiya da rikon amana. Yana da abubuwa da yawa na gani na yabawa, wanda lokaci ba zai ba mu damar rattabo su ba.
Har yanzu kana ci gaba da rubutun fina-finan Hausa, ko kuwa yanzu ka dakata, kasancewarka matsayin shugaban Kamfani?
Ina yi har yanzu, don yanzu haka ma akan wasu rubuce-rubucen nake.
Wanne fim ne wanda ka fara rubutawa, kuma wanne sako fim din ya isar?
‘Rintsin Kauna’ Sako ne akan wani Alhajin da ya mika wa matsafa wulayarsa kawai domin ya yi kudi, karshe kuma ya yi kudin amma kudin bai amfane su ba, ya mutu a wulakance har ma ya yi asarar surukinsa.
Ko za ka iya tuna adadin fina-finan da ka rubuta?
‘Dariya’ kai! ba zan iya ba wallahi, suna da yawa matuka.
Wanne fim ne a gaba daya rubutun da ka yi a rayuwarka ya fi baka wahala?
Ba a yi aikinsa ba, amma yana nan a rubuce kuma ni da Khalil Germany muka rubuta shi, a kalla ya dauke mu kwana 75 muna rubuta shi, kin ga kuma fim din da ba a yi shi ba ba a fadar sunansa saboda ‘yan satar fasaha.
A cikin Jaruman fina-finan Hausa da mawaka wa ya fi burgeka kuma me ya sa?
Gaskiya kin yi min tambaya mai wahala. A mawaka mata dai na fi son na ji wakar Murja Baba, domin tana da zalaka da fasaha, kuma tana iya sarrafa muryarta da numfashinta a koda yaushe. Mawaki kuma na fi son wakar Aminuddeen Ala saboda wakokinsa kusan dukkanninsu na fadakarwa ne. Amma a bangaren Jarumai a nan rigimar take, domin zai yi wahala ga mu marubuta ko ‘Producers’ mutum ya ware miki mutum daya wanda ya fi wani ko wanda ya fi burge shi, kasancewar ‘acting’ bangare-bangare ne, a kowane bangare ‘acting’ din wani ya sha banban da na wani. Za ki samu a bangaren ban dariya maganar wani ake yi, haka wanda ake magana a bangaren zalumci ba shi ake magana a bangaren soyayya ko daba ba.
Bayan harkar fim kana wata sana’ar ne?
Ni Ma’aikacin gwamnati ne.
Ya kake iya hada aikinka da kuma sana’arka ta fim?
Wannan shi ya fi komai sauki, lokacin aikin gwamnati ina ofis, lokacin aiki kuma ina wurin, ba na bari su yi karo da juna. Sa’annan kuma kin san ko’ina akwai mataimaka gudun ko-ta-kwana.
Mene ne burinka na gaba game da harkar fim?
Burina harkar fim ta zama sana’a a Nijeriya kamar yadda ta zama a India da Amurka.
Ya batun iyali fa, matanka nawa?
Matata daya jal, yarana 4, biyu mata sai maza biyu da suke biye musu.
Mene ne ra’ayinka game da kara aure, misali wata cikin masana’antar ta ce tana sonka, shin za ka amince ka aureta?
Gaskiya dayar ta ishe ni, ko ta binne ni, ko na binne ta, zan yi godiya sannan na yi mata addu’ar Allah ya ba ta miji nagari kamar yadda ya ba ni mata ta gari.
Wanne irin abinci da abin sha ka fi so?
A matsayina na Bahaushe dan bakin kasuwa na fi son Gurasa ko Alkubus. Sai kuma Kunu ko Koko da Kosai.
Wanne irin kaya ka fi son sakawa?
Na fi sanya doguwar riga da wando mai Tazuge.
Me za ka ce da masu yi wa sana’arku mummunan kallo?
Da farko ina yi musu uzuri kila rashin fahimta ne, ko rashin sanin yadda muke. Sa’annan ina rokonsu da su daure su yi bincike kafin su yi zargi ko furuci.
Wacce shawara za ka ba wa masu kokarin shiga harkar fim ko waka, har ma da wadanda ke ciki?
Su tsarkake niyyarsu, kuma su gamsu sana’a suke yi, sannan su toshe kunnuwansu, kuma su riki gaskiya da amana sannan su jajirce.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga gwamnati, game da harkar fim?
Kirana da gwamnati bai fice na gwamnati ta rika taimaka mana ba, musamman da jari da kuma kare mana fina-finanmu daga barayi da kuma gina mana ‘Flm Billage’.
Me za ka ce da masoyanka, da masu kallon fina-finanku?
Da farko ina yi musu godiya bisa kyakkyawar fahimtarsu gare mu, sa’annan muna cikin tsananin kishirwar bukatar addu’ar su, kuma a shirye muke da amsar gyaransu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Me za ka ce da shafin Rumbun Nishadi?
Duk wanda ya ji dadin abubuwan dana fada to yayi wa Allah godiya, domin hakan daga Allah ne. Wanda kuma ransa ya sosu kila domin na fadi wani abu na kuskure ko na fadi wani abu arashi a gare shi, ya yi min afuwa, kuskuren daga gare ni ne.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Abu biyu zan fada; Na farko ina addu’ar Allah ya kara daga darajar wannan jarida ta ci gaba da gabatar mana da abubuwan da za su amfane mu kamar yadda suka saba yi. Na biyu kuma ina fatan daga darajar Hajiya Rabi’at domin ban taba cin karo da dan jaridar da ya wahal da ni ba kamar ta. Na gode matuka.
Muna godiya kwarai da gaske, ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gai da dukkannin ‘yan uwana da iyalina da abokan sana’ata a Kannywood, Na gode.