Hukumar da ke kula kamfanoni a Nijeriya (CAC) da kamfanonin Fintech a Nijeriya da aka fi sani da masu POS sun cimma matsayar wa’adin wata biyu domin kammala rijistan wakilansu, ‘yan kasuwa da daidaikun masu hada-hadar kudaden da na’urar POS da hukumar CAC kamar yadda doka ta tanada da kuma umarnin yin hakan da babban bankin kasa (CBN) ya yi.
An kai ga wannan matsayar ne a yayin wata ganawa da ya gudana a tsakanin jami’an kamfanonin Fintech da babban rijista kuma babban jami’in gudunawar na hukumar CAC, Hussaini Ishak Magaji, SAN, a Abuja kwanakin baya.
- Wike Ya Ba Shugaban Ƙasar Sanigal Bassirou Faye Shaidar Zama Ɗan Ƙasa A Abuja
- Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Kaddamar Da Taron Koli Na LAS Karo Na 33
Da ya ke jawabinsa, shugaban CAC, Barista Hussaini Ishak Magaji, ya ce, babban manufar rijistan shine domin tabbatar da kare wa masu hada-hadar kudade ta POS kudaden su da inganta musu kasuwancinsu hadi da ganin an kyautata tattalin arziki.
Ya kara da cewa matakin ya samu marawar baya da sashi 863, karamin sashi na 1 na dokar kamfanoni CAMA 2020 hadi da ka’idojin CBN na 2013.
Hussaini Magaji daga nan ya ce za a kammala aikin rijistan masu POS a ranar 7 ga watan Yuli na 2024, da nufin tabbatar da kariya ga masu kasuwanci da POS.
Wadanda suka yi magana a madadin Fintech sun sha alwashin bada hadin kai ga hukumar domin cimma nasarar tsare-tsaren da ake da su.
Wasu daga cikin su kuma sun nuna bukatar da ke akwai a kara wayar da kai domin tabbatar cimma nasarar abubuwan da ake nema.
Shi kuma a nasa jawabin, Tokoni Igoin Peter, mai taimaka wa shugaban kasa kan ICT da kere-kere ya bada tabbacin bada hadin kai wajen samun nasarar da aka sanya a gaba domin cimma manufofin shugaban kasa na sabunta fata.
Wakilan OPAY, MOMBA, PALMPAYLTD, PAYSTACK, FAIRMONEY MFB, MONIEPOINT, da TEASY PAY sun sanya hannun nuna goyon baya ga shirin.
Ana dai yawan samun rahoton kesa-kesan damfara ta POS sama da sau 10,000 a cikin shekara guda.