Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya ta fito a cikin rukuni mai wahala a jada-walin wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na shekara ta 2025 da za a buga a kasar Morocco.
Sai dai da alama mai kare kambun gasar Nahiyar Afrika, wato Ibory Coast, za ta iya kaiwa ga gasar ta 2025 da za a yi a Morocco, amma da alama Nijeriya ta fada wani rukuni mai matukar rintsi da wahala.
Raba rukunin da aka yi a Birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, tawagar Super Eagles ta tsinci kanta cikin rukuni daya da kasashen Benin da Rwanda da kuma kasar Libya.
Yanzu tsohon kocin Nijeriya Gernot Rohr ne ke horar da Benin, kuma ya doke Nijeriya da ci 2-1 a watan jiya a wasannin share fagen shiga gasar kofin duniya ta shekarar 2026.
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya yanzu na neman sabon koci biyo bayan ajiye aikin da Finidi George ya yi wanda ya koma Ribers United. Sai dai har yanzu hukumar kwallon kafa ta kasar ba ta tabbatar da tafiyarsa ba a hukumance.
Ibory Coast da ta lashe gasar nahiyar karo na uku bayan doke Nijeriya a wasan karshe a watan Fabirairu, za ta fafata da gwarzuwar gasar 2012 Zambia, Sierra Leone da kuma Chadi.
Kocin tawagar Ibory Coast, Emerse Fae ya taimaka wajen raba rukunin da aka yi a Jo-hannesburg kuma ya yi farin ciki da sakamakon inda ya ce sun yi wasa da Zambia a wasan share fagen AFCON na baya, saboda haka sun san tawagarsu sosai da sosai.
Tawagar kasashe 48 din an raba su zuwa rukunai 12 ne zuwa kuma gida hudu, yayin da tawagogi biyu na kowanne rukuni za su samu zuwa Morocco a karshe domin buga gasar.
Masu masaukin baki na da kujerar dindindin a gasar, don haka tawaga daya ake nema a rukunin da suke, wanda ya hada da Gabon, Central African Republic da kuma Leso-tho.
Kamar yadda hukumar kula da gasar cin kofin na Afirka ta tsara, za a yi wasanni shida ne na neman gurbin a watan Satumba da Oktoba da kuma watan Nuwambar wannan shekarar. Za a fara wasan AFCON 2025 a ranar 21 ga watan Disambar shekara mai
zuwa, a kuma yi wasan karshe na gasar a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2026 kamar yadda aka tsara.
Gasar za a buga ta ne lokacin da ake wasannin Firimiyar Ingila na karshen shekara da kuma gasar cin kofin zakarun Turai, sannan wannan ne karon farko da ake buga gasar a watan Nuwamba a tarihi, kuma zai shiga lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Rukunan samun shiga Afcon 2025
Rukunin A: Tunisia, Madagascar, Comoros, The Gambia.- Rukinin B: Morocco, Ga-bon, Central African Republic, Lesotho.- Rukinin C: Egypt, Cape Berde, Mauritania, Botswana.
Rukinin D: Nigeria, Benin, Libya, Rwanda.- Rukinin E: Algeria, Ekuatorial Guinea, To-go, Liberia.- Rukinin F: Ghana, Angola, Sudan, Nijar.- Rukinin G: Ibory Coast, Zambia, Sierra Leone, Chad.- Rukinin H: DR Congo, Guinea, Tanzania, Ethiopia.- Rukinin I: Mali, Mozambikue, Guinea-Bissau, Eswatini.- Rukinin J: Kamaru, Namibia, Kenya, Zimbabwe.- Rukinin K: South Africa, Uganda, Congo, South Sudan. Rukinin L: Senegal, Burkina Faso, Malawi, Burundi