Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta dage wasan tawagar Super Eagles da tawagar kasar Libya, wanda ya shirya yi a ranar Talata.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ba za a fafata wasan ba, kamar yadda aka shirya fafatawar ba.
- Dole Ne A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro
- Li Qiang Ya Kai Ziyarar Aiki Pakistan Tare Da Halartar Taron Kwamitin Shugabannin Gwamnatocin Kasashe Mambobin Kungiyar SCO Karo Na 23
An shirya fafata wasan ne na rukunin D a filin wasa na Martyrs of Benna da ke Benghazi, kafin tsaikon tarbar tawagar Nijeriya a kasar ya haifar da ce-ce-ku-ce, har ‘yan wasan Nijeriya suka koma gida.
Wannan matakin na CAF ya kwantar da fargabar da ake yi na kasar da za a ba nasarar a wasan, inda wasu magoya bayan wasan Super Eagles suka yi fargabar za a ba Libya nasara a wasan da ci uku da nema, kamar yadda ake yi idan abokin kara wa bai zo ba.
CAF ta ce ta tura lamarin zuwa kwamitin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace, tare da sanar da ranar da za a fafata wasan.