Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), ta yi Allah wadai da yunkurin kashe babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Bauchi kan harkokin addinin Kirista, Fasto Zakka Magaji da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi.
Shugaban kungiyar CAN a jihar, Rabaran Abraham Damina Dimeus, ya yi Allah wadai da harin da aka kai a ranar Juma’a a lokacin da ya jagoranci jami’an kungiyar a ziyarar jaje zuwa gidan hadimin gwamnan da ke Birshi.
- FBI Na Neman Wani Dan Nijeriya Da Ya Damfari Amurka Dala Miliyan 30
- ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Hadimin Gwamnan Bauchi, Sun Jikkata Mutum 1
Dimeus wanda ya ce ba a san dalilin kai harin ba ya yi wa’azin cewa ya kamata mutane su sani cewa rayuwa tana da tsarki kuma dole ne a kiyaye ta ko ta halin kaka.
Yayin da ya ke godewa Allah da cewa ba a samu asarar rai ba yayin harin, ya kuma jaddada bukatar karfafa tsaro a kasar.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakan tsaro musamman a yankunan da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.
Limamin ya ce ya kamata a kara kaimi domin ceto al’amuran tsaro a kasar.
Dimeus ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da tsaro da kuma bayanan sa kai domin kama bata-gari a cikin al’umma.
Idan dai za a iya tunawa da sanyin safiyar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan babban mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Bauchi kan harkokin addinin Kirista, Fasto Zakka Luka Magaji, a wani yunkurin sace shi da ba su yi nasara ba.