Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ce yana sane da irin bakar wahalar da jama’a ke ciki wanda canjin kudi ya haifar.
Buhari ya sanar da hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Juma’a.
- Ana Gab Da Gabatar Da Kumfyutar Quantum Na Sin Mai Suna Wukong
- Mulkin Nijeriya Ya Bambanta Da Mulkin Jiha, Shi Ya Sa Atiku Ya Fi Tinubu Cancanta -Saraki
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da Buhari ya yi da gwamnonin APC, inda suka roke shi kan yadda za a saukaka wa talakawa halin da suka shiga a sanadin canjin kudin.
“Ina sane da karancin kudi da wahalar da mutane da ‘yan kasuwa ke fuskanta sakamakon canjin kudi ya haifar. Ina tabbatar da cewar za mu yi duk mai yiwuwa don saukaka halin da aka tsinci kai a ciki. Daga nan zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, ‘yan Nijeriya za su ga sauyi sosai.
“Na gana da gamayyar gwamnoni yau a kan matsalar. Dukkanin korafin da aka gabatar za a duba su domin kawo sauyi.
“Zan tabbatar da cewar an warware komai cikin sauki sannan zamu dade muna cin moriyar wannan hukunci da aka zartar,”in ji Buhari.
Tun bayan da aka sauya fasalin takardun kudi mutane da dama sun shiga wahala, lamarin da ya kai wasu daina kasuwancinsu sakamakon rashin kudi a hannun mutane.