Babban Bankin Nijeriya CBN ya ba bankunan da ke fadin ƙasar umarnin daina bayar da sabbin kuɗi kai-tsaye ga kwastomomin da suka shiga cikin banki don karɓar kuɗi.
CBN ya buƙaci bankunan da su saka sabbin kuɗin cikin na’urorinsu na cirar kuɗi na ATM Don tabbatar da kuɗin ya shiga hannun jama’a gabanin ranar da wa’adin zai kare ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki na daina amfani da tsohon kuɗin.
- Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Ba Mu San Adadin Sabbin Kudin Da Muka Buga Ba – CBN
Umarnin babban bankin ya ya bukaci bankunan da su gaggauta aiwatar da wannan tsarin.
Cikin watan Oktoban da ya gabata ne Bankin CBN, ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗe a Nijeriya tare da umartar mutane da su mayar da tsofaffin kudaɗen banki don sauya musu da wasu sababbi.