Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fitar da jerin sunayen bankuna 41 da ya aminta da ingancinsu a fadin kasar nan.
Bankunan dai CBN wadanda ne ya ba su lasisin izinin gudanar da ayyukansu a ciki da wajen kasar nan.
- Gwamna Nasir Ya Bada Gudunmuwar Naira Miliyan 100 Ga Kungiyar Lauyoyi Kan Gina Sakatariya A Kebbi
- CBN Ya Bukaci Masu POS Su Yi Rajista Da Gwamnati
CBN ya wallafa sunayen wadannan bankunan ne a shafinsa na Intanet a ranar Talata.
Bankunan da ke da izinin kasa da kasa su ne kamar haka:
- Access Bank
- Fidelity Bank
- First City Monument Bank
- First Bank Nigeria
- Guaranty Trust Bank
- United Bank of Africa Plc, da Zenith Bank Plc
Bankunan kasuwanci masu izini a cikin kasa su ne kamar haka:
- Citibank Nigeria
- Ecobank Nigeria
- Heritage Bank
- Globus Bank
- Keystone Bank
- Polaris Bank
- Stanbic IBTC Bank
- Standard Chartered Bank/ Sterling Bank
- Titan Trust Bank
- Union Bank
- Unity Bank
- Wema Bank
- Premium Trust Bank
- Optimus Bank
Bankunan kasuwanci masu lasisin yanki sun hada da:
- Providus Bank
- Parallex Bank
- Suntrust Bank Nigeria
- Signature Bank
Bankunan da ba sa karbar kudin ruwa masu izini a Najeriya su ne:
- Jaiz Bank
- Taj Bank
- Lotus Bank
- Alternative Bank
Nau’in bankunan hada-hadar kasuwanci da suka hada da:
- Coronation Merchant Bank
- FBN Merchant Bank
- FSDH Merchant Bank
- Greenwich Merchant Bank
- Nova Merchant Bank
- Rand Merchant Bank
Bankunan da ke wasu harkokin daban bayan na kudade:
- Access Holdings
- FBN Holdings
- FCMB Group
- FSDH Holding Company
- Guaranty Trust Holding Company
- Stanbic IBTC Holdings
- Sterling Financial Holdings