Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayar da lambobin waya da imel domin mutane su rika bayar da rahoton matsaloli da suka shafi karancin kudi a na’urar ATM.
Wannan matakin, wanda aka sanar a ranar 29 ga watan Nuwamba, yana da nufin inganta samun kudi da tabbatar da zagayawar kudi a hannu jama’a.
- An Kashe ‘Yansanda 229 Cikin Watanni 22 A Nijeriya – Rahoto
- Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Shari’a Da Majalisa Su Yi Aiki Tare Kan Dokar Haraji
CBN ya umarci bankuna su bai wa tsarin fifiko wajen saka a kudi a ATM da wuraren karbar kudi, tare da gargadin cewa duk wani banki da ya yi kunnen uwar shegu dokar zai fuskanci hukunci.
CBN ya ce hakan zai karfafa alaka tsakaninsu da kwastommi ta hanyar bayar da rahoton matsaloli tare da bayanai kamar sunan asusu, sunan banki, adadin kudi, da lokacin da abin ya faru.
Ana iya aika rahoton zuwa ofishin CBN na kowace jiha d matsalar ta faru ko ta hanyar imel.
CBN ya ce wadannan matakan za su taimaka wajen magance matsalar rashin kudi da inganta yanayinsu a fadin Nijeriya.