A ci gaba da tsaftace Bankunan kasa, Babban bankin Nijeriya (CBN) ya ruguza shugabannin gudanarwar bankunan Titan Trust da Polaris da Union Bank da Keystone.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, matakin na ruguza shugabannin ya biyo bayan wani rahoton bincike na musamman da wani mai bincike (Jim Obaeze) ya gudanar kan babban bankin Nijeriya (CBN).
A yammacin yau Laraba ne dai ake sa ran CBN zai fitar da cikakkiyar bayanan dakatarwar da kuma sauye-sauyen da aka samu, bayan wata ganawa da gwamnan babban bankin na CBN, Yemi Cardoso; da mai binciken, Obazee; da kuma shuwagabannin da ke kula da bankunan da abin ya shafa.
Cikakken bayanai na zuwa daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp