Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sauya tsarin cajin ATM, inda ya soke damar cire kuɗi kyauta sau uku a wata daga ATM na wasu bankuna.
Wannan sabon tsari, wanda za a fara aiwatarwa daga 1 ga Maris, 2025, ya bayyana ne a wata sanarwa da Daraktan riƙo na sashin tsare-tsaren kuɗi da dokoki, John Onojah, ya fitar.
- Bankin Duniya Da IMF Sun Buƙaci CBN Ya Daƙile Hauhawar Farashi A Nijeriya
- CBN Zai Mayar Wa Da Masu Musayar Kudi Kudin Da Suka Biya Na Lasisi A 2025
CBN ya bayyana cewa sauya dokar na da nufin inganta ayyukan ATM da rage farashin gudanarwa a bankuna.
Sabbin dokokin sun haɗa da:
Cire kudi daga ATM na bankinka: Za a ci gaba da yin hakan kyauta.
ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000.
ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500.
Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata.
CBN ya ce wannan sabon tsari zai ƙarfafa shigar da sabbin ATM a faɗin ƙasa tare da tabbatar da cewa bankuna suna cajin kuɗin da ya dace.