Bayan shafe mako daya da fara aiki, hukumar kula da da’ar ma’aikata CCB ta kafa wani kwamiti don tantance asusun ajiya a bankuna da kuma kadarorin sabbin ministocin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada.
Kazalika, tawagar za ta kuma tantance kadarorin da gwamoni suka yi ikirarin sun mallaka da kuma kadarorin wadanda aka nada a mukaman siyasa a matakan jihohi da na kananan hukimomi da kuma a matakin tarayya.
- Zargin Rashin Kammala Hidimar Kasa: Babu Dokar Da Ta Hana A Nadani Minista – MusawaÂ
- Tinubu Ya Bukaci Sabbin Ministoci Kan Su Yi Aiki Tukuru Don Biyan Bukatun ‘Yan Nijeriya
Hukumar za ta gudanar da wannan aikin ne tare da hadin guiwar sashin da ke sa ido akan hada-hadar kudi na kasa NFIU da bankuna da hukumar da ke yin rijistar kasuwanci CAC da hukumar kula da musayar hada-hadar kudade SEC da hukumar yin rijistar gidaje da kuma hukumomin da ke yi wa ababen hawa rijista.
Bincike da aka gudanar ya nuna cewa, jerin asusun ajiya na bankuna da kuma na kadarorin da ministocin suka mallaka, an tura wa hukumar ta CCB da kuma sauran hukumomi domin a tabbatar da ikirarin na gwamoni da ministocin da kuma sauran wadanda aka nada a mukaman na siyasa.
An rawaito cewa, aikin na tantancewar kwamitin zai gudanar zai iya shafe watanni ana gudanar da shi.