An nada tsohon kocin Italiya, Roberto Mancini a matsayin sabon kocin Saudiyya.
Tsohon kocin na Man City, mai shekaru 58 ya bar aikinsa na kocin Italiya makonni biyu da suka gabata.
- CAF Champions League:An Fitar Da Kungiyoyin Najeriya Dake Buga Gasar
- Nunez Ya Ci Kwallo 2 A Minti 10 Yayin Da Liverpool Ta Doke Newcastle
Sai dai a yanzu hukumar kwallon kafa ta Saudiyya ta bayyana dan kasar Italiya a matsayin kocinta a wani faifan bidiyo ta yanar gizo.
Talla
Rahotanni sun bayyana cewa Mancini ya sanya hannu a kan kwantiragin fam miliyan 77 na tsawon shekaru uku.
Za a bayyana shi a wani biki mai kayatarwa a Riyadh ranar Litinin, a cewar Gazzetta dello Sport.
Wasansa na farko da zai jagoranci kasar zai kasance ne da Costa Rica a wasan sada zumunci a St James Park ranar 8 ga watan Satumba.
Talla