A kwanan baya ne, Hukumar Raba daidai ta ƙasa, ta shelanta cewa, za ta yiwa ƴ an siyasa, masu riƙe da
madafun iko, ƙarin albashin, inda wannan batun, ya haifar da ce-ce kuce da kuma suka daga ɓangarori da
dama, na ƙasar.
Sukar dai, ta biyo bayan ganin cewa, ƙarin bai da ce, duba da irin matsin tattalin arziki, da ya yiwa ƙasar
ɗaurin Demom Minti da ci ga da fuskatar hauhawan farashin kayan masarufi, musamman kayan abinci da
giɓin da aka samu, a cikin kasafin kuɗin ƙasar da kuma irin halin ƙunci rayuwa, musamman da talakawan ƙasar, suka tsinci kansu a ciki.
- Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Nijeriya Sun Koka Kan Rashin Biyan Basussukan Albashi
- Manyan Jami’ai A Ma’aikatar Tsaro Ta Cikin Gida Za Su Ci Gaba Da Karɓar Albashi Har Ƙarshen Rayuwa
Sai dai, Hukumar ta kafa hujja da cewa, ƙarin ya zama wajibi, musamman domin tun a shekarar 2008, shugaba ƙasa har yanzu, na karɓar Naira miliyan 1.5 a duk wata, a matsayin albashi inda ministoci, ke karɓar ƙasa da Naira miliyan ɗaya, a duk wata, a matsayin albashi.
Kazalika, Hukumar ta tage kai da fata cewa, wannan jeren albashin, ya yi ƙaranci matuƙa, duba da
hauhawan farashin kaya a ƙasar da kuma tsadar rayuwa.
A cewar Hukumar akwai matuƙar banbanci kan albashin da ake biyan masu riƙe da madafun ikon na
siyasa, da kuma na sauran shugabannin Hukumin Gwamnati, musamman dai, albashi kamar na Darakta- Janar da na cibiyoyin kuɗi, kamar irinsu Babban Bankin Nijeriya, waɗanda albashinsu, ya ɗara na
shugaban ƙasa da kuma na ministoci.
Amma wannan ya nuna cewa, akasarin masu riƙe da madafun ikon na siyasa, a ƙasar, sun fi samun kuɗaɗen shiga ne ta hanyar alawus-alawus da suke samu.
Misali, a duk wata, Sanata ɗaya na samun alawus da ya kai sama da Naira miliyan 21, wasu ƴ an majlisar, a shekara ɗaya, suke samun alawus da ya kai na Naira 500 da sunan na ayyukan da suke gudanarwa, a
mazaɓunsu, wanda ba a sanya wannan, a lissafi.
Bugu da ƙari, akwai kuma sauran wasu kuɗaɗen shiga da ƴ an siyasar, masu riƙe da madafun iko suke samu, waɗanda suka haɗa da na gidajen kwanansu da na tafiye-tafiyensu da na tsaronsu da kuma na sauran wasu damarmaki, wanda wannan, ya ɗara kuɗaɗen shiga, da ma’aikatan gwamnati suke samu da kuma na sauran fannoni da ban da ban.Wannan batun na cewa, ana biyan ƴ an siyasar masu riƙe da madafun ikon, kuɗaɗen da ba su taka Kara sun karya ba, za a iya cewa, wani yunƙuri ne, na karkatar da kan alumma da kuma yunƙurin chusawa, ƴan Nijeriya, rashin yarda a Zukakansu. A zahirance, tuni a Nijeriya aka mayar da muƙaman siyasa zuwa wata haynya ta hada-hadar cinikayya,
mai makon a mayar da hankali, wajen inganta rayuwar ƴ an ƙasa.
Hakan ne ya ke sanya, ko ta halin ƙaƙa, a lokacin da ta zaɓe ya ƙarato, wasu masu son sake ci gaba da riƙe muƙamansu, suke tayar da hargitsi ko kuma kashe ɗimbin biliyoyin Naira, domin kawai, su sake
lashe zaɓe.
A daidai wannan lokacin ne, da Hukumar ke son ganin an yiwa ƴ an siyasar masu riƙe da madafun ikon,
hakan ya zaburar da ƙungiyoyi kamar su na ƙwadago da ƙunƙiyar tuntuɓa ta Arewacin ƙasar wato ACF da ƙungiyar da ke kare muradun jama’ar Arewa ta tsakiya wato MBF, suka fara yin suka da kuma yin tir, kan wannan yunƙurin na ƙarin wanda suka alƙanta shi, a matsayin son rai da nuna handama.
Kazalika, masu sukar na ganin cewa, gwamnatin ta yi watsi da irin halin ƙuncin rayuwa da musamman
talakwan ƙasar, ke ci gaba da fuskanta, kamar dai, na ci gaba da hauhawan farashin kayan masarufi da
ƙarin kuɗin Man Fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki da ƙarancin albashin da ake biyan ma’aikata, musamman na gwamnati, wanda a baya, ta yi alƙawarin lalubo masu da mafita.
Wannan batun na ƙarin albashin, tamkar dai wani cin zarafi wanda kuma abu ne, da ke tattare da hatsari.
Kusan tun lokacin da shugaba Bola Tinubu, ya ɗare Karagar shugabancin ƙasar, ya rage yawan kuɗaɗen
da ake kashewa, na gudanar da mulki, inda gwamtainsa, ta rage yawan ɗimbin tawagar da take kwasa, na
yin tafiye-tafiye, musamman zuwa ƙasashen duniya.
Amma batun na ƙarawa ƴ an siyasa masu riƙe da madafun ikon, a wannan yanayin da ƙasar ke a ciki, tamkar mayar da Agogo baya ne.
Misali, gwamnatin har zuwa yau, ta gaza wajen cika ɗaukacin buƙatun ƙungiyoyin manyan makaratun
ƙasar wato ASU da kuma ASUP, inda kuma a gefe ɗaya, ƙungiyoyin ƙwarrun likitoci, suma suke ta kai gwauro da mari, na neman gwamnatin, ta biya masu na su buƙatun
Saboda rashin biya masu buƙatun na su, suke tsunduma cikin yajin aiki na gargaɗi ko kuma gargaɗi.
Hakazalik, a yayin da ƙasar ke jigelon kashe kuɗaɗe, na gudanar da wasu ayyuka a ƙetare, amma a gife
ɗaya, an bar ma’aikata na karɓar mafi ƙarancin alabshin na Naira 70,000 kacal, inda wannan kuɗin, ba zai
iya kawar masu koda da ƙishirwarsu ba, duba da hauhawan kayan masarufi, da ake ci gaba da fuskanta a
ƙasar.
Akasarin ma’aikata a ƙasar, na ci gaba da kasance wa ne a cikin talauci, inda kuma sauran ƴ an siyasa, ke ci gaba da yin wadaƙa.
Maimakon ƙarin albashin kamata yi Hukumar ta fara tunanin fara yiwa albashin ma’aikatan gwamnati
garanbawul da kuma inganta rayuwarsu.A yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙaranci kuɗi tare da kuma yadda alummar ƙasarke ci gaba da
fitar da rai ga alƙawarin da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi, na saita ƙasar, batun na yin ƙarin, a wannan
lokacin, wani abin dubawa ne.
Wannna Jaridar ta nuna takaicinta kan wannan batun, musamman duba da cewa, yunƙurin na Hukumar, na ci gaba da fuskantar suka.
Bugu da ƙari, duba da cewa, Nijeriya kusan ta dogara ne kachokam, kan ciwao bashi daga ƙetare, domin
ci giɓin da take da shi, a cikin kasafin kuɗinta, wanda hakan ya saɓawa ƙa’ida, a saboda haka, batun na
ƙarin albashin ga ƴan siyasa, tamkar zuba kuɗi ne, a inda bai kamata ba.
Ya zama wajibi, gwamnatin ta dakatar da wannan batun na ƙarin albashin ga ƴan siyasa masu riƙe da madafun iko, amma ta mayar da hankali, wajen gudanar da bin diddigin kashe kuɗaɗe wanda zai yi daidai da, tsarin tattalin arzikin ƙasar, a zahirance da kuma gudanar da ƙa’idojin gudanar da aikin gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp