• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ce-ce-kucen Al’umma Ke Ci Wa Mawakan Kannywood Tuwo A Kwarya —Jibrin Yahaya

by Rabi'at Sidi Bala
3 years ago
Jibrin Yahaya

A wannan makon mun kawo maku cigaban tattaunawar da muka kawo muku a fitowarmu ta makon da ya gabata. Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo maku fitattun jarumai, har ma da masu tasowa daga cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Tare da manyan mawaka har ma da kanana, kana da wadanda suka yi fuce. A yau ma shafin na tafe da bako na musamman wanda ya shafe tsahon shekaru goma a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Jarumi mai taka rawa da kuma shirya fina-finai cikin masana’atar kannywood, kana shahararren mawakin wakokin Hausa da suka shafi kowanne bangare. JIBRIN YAHAYA wanda aka fi sani da MISTER D MAIWAKA, Ya bayyanawa masu karatu musabbabin fara wakarsa tare da dalilansa na shiga masana’antar Kannywood, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta fim. Ga dai yadda tattaunawar tasu da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Kana fidda bidiyos ne ko iya odiyo kake yi ?
Ina fidda ‘Audio’ da kuma Bidiyo.

Idan mutum yana son samun wakokinka ta wacce hanya zai nema?
Wakokina za a same su a ‘Youtube Channel’ dina mai suna ‘MD 24 TB’ ko a WhatsApp line kamar haka 08029157961 ko wurin ‘yan ‘Download’.

Wacce irin matsala kake fuskanta game da harkokin fina-finanku da kuma bangaren waka?
Matsala ba ta wuce ce-ce-ku-ce na mutanan gari wanda shi daman dan Adam ba a iya masa, kuma duk abin da za ka yi in kai bawa ka tsarkake zuciyarka duk abin da mutum zai fada yai ta fada domin Allah na kallon mu kuma zai wa bawa a kan aibata wanda ya ke yi.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Me za ka ce da su masu ce ce-ku ce a kanku?
Kalma daya ce su daina, hakan ba daidai bane. Domin ko da mutum bai haifa ba ‘yan uwansa sun haifa, kuma duk abin da kai za a yi ma wani, kairan o sharren.

Toh! Ya batun aure fa?
Ina da aure, Allah ya azurta ni da ‘ya’ya hudu, daya ta rasu Allah ya ji kanta. Uku na raye Khalid da Auwal, sai Fatima, Allah ya albarkace su Ameen.

Shin ka taba fuskantar wani kalubale daga wajen matarka game da aikinka, musamman ma yadda jama’a ke kallon yanayin aikin na cakude da wasu matan daban?
Gaskiya so daya na taba haduwa da hakan, shi ma ba wai na bacin rai bane, wani lokacin ne aka je aka ce da ita gani can da mata sai ta ce hanyar cin abincin sa ce a haka, Allah da ikonsa ni dai ban taba jin an ce gashi can an kama shi da wata mace ba, na ga a cikin garin nan kuma wanda baya fim ko waka an kama shi da mace ba. ita ta gayan ba matar aboki na ce take gaya min har ita ma matar abokin nawa ta ce ‘hanyar cin abincin sa ce a haka kuma ko wane bawa baya tsallake kaddarar sa.

Mene ne burinka na karshe a rayuwa?
Shi ne na gama da duniya lafiya.

Me za ka ce da makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Su ci gaba da kasancewa tare da wannan shafi, domin karanta gaskiyar zance game da Jarumi ko Jaruma haka ma mawaka, domin shafi ne da yake fidda masu kallo daga cikin duhun ka ce na ce akan jarumi, irin na wasu mutanen.

Me za ka ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina yi mata fatan alkhairi, ubangiji ya kara daukakata ya sa ta fi haka, ya karawa ma’aikatanta hazaka da basira.

Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Kwarai kuwa, sai dai amma suna da yawa ba zan iya fado su ba, zan yi su a dunkule, bayan gaisuwa ga dukkanin iyayena, ‘yan uwana, da matata da kuma iyalaina baki daya, ina gaida duk wadanda suka zamo na kusa da ni abokaina da kuma masoyana a duk inda suke, da sauran al’ummar musulmi baki daya.

Muna godiya ka huta lafiya.
Ni ma na gode.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Nishadi

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Next Post
Babban Mai Tattara Sakamakon Zaben Atiku A Ogun Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Babban Mai Tattara Sakamakon Zaben Atiku A Ogun Ya Sauya Sheka Zuwa APC

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.